1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta hana Ousmane Sonko takara a Senegal

Suleiman Babayo AH
January 6, 2024

A kasar Sengal majalisar tsarin mulkin kasar ta bayyana yin yi watsi da takara na neman shugabancin kasar na jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko saboda rashin cika sharuda da aka tsara.

https://p.dw.com/p/4aukJ
Madugun adawa a Senegal, Ousmane Sonko
Madugun adawar kasar Senegal, Ousmane Sonko Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Kotun tsarin mulkin kasar Senegal, ta ki amincewa da takarar madugun adawar kasar Ousmane Sonko a zaben shugaban kasa da za a yi cikin watan gobe na Fabrairu.

Ousmane Sonko mai shekaru 49, wamda ya zo na uku a zaben shekarar 2019 dai fitaccen mai hamayya ne da gwamnatin Senegal din.

Lauyansa da ya tabbatar da batun hana shi takarar da aka yi, ya ce madogara kotun ita ce Ousmane Sonkon bai cike sharudan da za su ba shi damar tsayawa takara ba.

Cikin watan Yulin bara ne dai Shugaba Macky Sall na Senegal ya sanar da cewa ba zai tsaya takara a zaben ranar 25 ga watan Fabarirun ba, inda ya tsayar da Firaminista Amadou Ba.

Sama da masu neman takara 90 ne dai suka mika sunayensu ga kotun na tsarin mulki, inda ake sa ran ta bayyana su a ranar 20 ga wannan wata na Janairu.