1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macky Sall na Senegal ba zai yi tazarce ba

Mouhamadou Awal Balarabe
July 4, 2023

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce ba zai sake tsayawa takara a karo na uku ba, sakamakon cece-kuce da aka shafe watanni ana yi game da alamunsa na neman yin tazarce. Yana mulki a Senegal tun 2012.

https://p.dw.com/p/4TNaE
Macky Sall ya ce ba zai nemi sabon wa#adin mulki a Senegal baHoto: John Thys/AFP

A wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar talabijin, Sall mai shekaru 61 da haihuwa ya ce duk da cewa kundin tsarin mulkin Senegal ya ba shi dama, amma ba ya so ya zama silar haddasa tashin hankali a kasarsa, saboda ba zai sake tsayawa takara ba.

 Da farko dai 'yan adawa sun yi imanin cewa shugaban zai sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na 25 ga Fabrairu 2024, lamarin da suke ganin cewa ya saba wa kundin tsrain mulkin kasar. Shi dai Macky ya dare kan kujerar mulkin kasar Senegal da ta yi fice a fannin mutunta dimokuradiyya a yammacin Afirka tun shekara ta 2012 wato shekaru 11 da suka gabata.

Amma watan Yuni, Senegal ta fuskanci munanan tarzoma bayan da aka yanke wa madugun 'yan adawa Ousmane Sonko hukuncin dauri a gidan yari bisa laifin tunzura matasa ga yin bore, lamarin da ka iya hana masa tsayawa takara.