1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Benin

April 27, 2024

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da kungiyoyin kwadagon Jamhuriyar Benin suka kira kan tsadar rayuwa da kuma yanayin tafiyar da gwamnati.

https://p.dw.com/p/4fG2I
Masu zanga-zanga a birnin Cotonou na kasar Benin dauke da kwalaye
Masu zanga-zanga a birnin Cotonou na kasar Benin dauke da kwalayeHoto: Abadjaye Justin Sodogandji/AFP/Getty Images

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana cewa 'yan sanda sun tarwatsa wasu gungun mutanen da ke gudanar da zanga-zangar a babban birnin kasar.

Karin bayani: Jamhuriyar Benin ta sake bude kofofinta ga 'yan Nijar

Kazalika guda daga cikin masu zanga-zangar Ariane Assilamehou ta shaidawa AFP cewa 'ta zo ne domin shiga gangamin yaki da tsadar rayuwa, amma 'yan sanda sun hana su rawar-gaban hantsi wajen harbin su da barkonon tsohuwa.

Karin bayani: Benin ta janye haramcin da ta yi wa Nijar na fiton kayayyakinta ta gabar ruwan Cotonou

Babbar kungiyar kwadagon kasar ta Benin CSA ta ce 'yan sanda sun yi awon-gaba da shugaban kungiyar Anselme Amoussou. 'Yan sanda sun ki cewa uffan dangane da wannan al'amari na murkushe masu zanga-zangar tsadar rayuwa a gwamnatin shugaba Patrice Talon.