1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wutar lantarki: Ministan makamashin Saliyo ya yi murabus

April 27, 2024

Ministan makamashi na kasar Saliyo Alhadji Kanja Sesay ya ajiye aiki sakamakon yawaitar daukewar hasken wutar lantarki da ake fuskanta a kasar, acewar sanarwar fadar shugaban kasar da ke birnin Freetown.

https://p.dw.com/p/4fFNQ
Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio
Shugaban kasar Saliyo Julius Maada BioHoto: Ali Balikci/AA/picture alliance

Tun bayan dankwafar da shahadar aikin, ministan Alhadji Kanja Sesay, yaki cewa uffan dangane da murabus din da yayi tare da kin amincewa da bukatar tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Karin bayani: 'Yan sandan Saliyo sun zargi tsohon shugaban kasa Ernest Bai Koroma da kitsa juyin mulki

Tsohon ministan na makamashin kasar ta Saliyo na aiki ne karkashin kulawar shugaban kasar Julius Maada Bio tare da wasu mutanen biyu, acewar sanarwar murabus din ministan da hukumomin kasar suka bawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Karin bayani: An bude wuta a gidan yarin Saliyo 

Murabun din ministan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Saliyo ta rattaba hannu kan kwangilar Dalar Amurka milyan 18.5 da wasu kamfanonin kasar Turkiyya guda biyu domin samar da hasken wutar lantarki a fadin kasar.