1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta bukaci karin takunkumai a kan Rasha

Binta Aliyu Zurmi
April 5, 2022

Shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky ya bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki tsauraran matakan ladabtarwa a kan Rasha bisa kisan gillan wasu fararen hula.

https://p.dw.com/p/49VmO
UN-Sicherheitsrat tagt zur Ukraine | Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Spencer Platt/Getty Images/AFP

Shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky a wata ganawa da ya yi da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kwamitin da ya gagauta hukunta dakarun sojin kasar Rasha a kan abin da ya kira aikata laifukan yaki a kan fararen hula.

Shugaba Zelensky ya ce abin da sojojin Rasha suka aikita a kan al'ummar garin Bucha abu ne da ba a ga irin shi ba tun bayan yakin duniya na biyu. Kazalika ya kwantanta wannan aika-aikan nasu da ayyukan mayakan kungiyar IS da ke ikirarin jihadi.

A tattaunawar da ta wakana ta kafar bidiyo, shugaban na Ukraine ya roki kwamitin na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi la'akari da shaidun da ake kara samu a kan kisan gillar da sojojin suka yi na kara wa kasar Rasha wasu tsauraran takunkumai.

Dama dai ko kafin wannan zama da shugaba Zelensky ya yi da kwamitin, babban sakatare na kungiyar tsaro ta Nato Jens Stoltenberg ya sha alwashin karin wasu takunkumai ga kasar Rasha da ma taimakawa Ukraine da karin wasu manyan makamai da za ta ci gaba da kare kanta a yakin da take yi da kasar Rasha.