1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tunisa da Algeria da kuma Libya sun kafa sabuwar hadaka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 23, 2024

Kasashen sun kuduri aniyar gudanar da taron a duk bayan watanni uku, don nazartar matakan tsaro a kan iyakokinsu da harkokin tattalin arziki da siyasa, da kuma duk wani sha'ani da ya shafi ci gaban kasashen uku

https://p.dw.com/p/4f4tV
Hoto: Elenathewise/Fotolia

Kasashen Tunisa da Algeria da kuma Libya sun gudanar da wani taro irin sa na farko a birnin Tunis, da nufin samar da shawarwarin kirkiro sabuwar gamayyar jan ragamar gudanar da harkokin kula da yankinsu na Maghreb, to sai dai ba a ga kasashen Morocco da Mauritania a taron na ranar Litinin ba.

Karin bayani:An rantsar da mukaddashin shugaban kasar Tunisiya

Ministan harkokin wajen Tunisia Nabil Ammar, ya ce kasashen sun kuduri aniyar gudanar da taron a duk bayan watanni uku, don nazartar matakan tsaro a kan iyakokinsu da harkokin tattalin arziki da siyasa, da kuma duk wani sha'ani da ya shafi ci gaban kasashen uku.

Karin bayani:Zanga-zangar matasa a arewacin Afirka

Taron ya samo asali ne lokacin da shugaba Abdelmajid Tebboune na Algeria da takwaransa na Tunisia Kais Saied da kuma jagoran gwamnatin Libya Mohamed Al-Menfi suka hadu da juna, yayin taron kasashe masu arzikin makamashin Gas karo na 7 da aka gudanar a cikin watan Maris din da ya gabata a Algeria.

To sai dai Morocco ta yi shaguben cewa Algeria ta kitsa taron ne don zama kishiyarta, ta hanyar cike gurbin kungiyar hadin kan kasashen Larabawan Maghreb da aka kirkiro a Morocco a shekarar 1989.