1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa Tsakanin Gwamnatin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Tarrayar 'Najeriya ta cije

January 15, 2012

Ba a cimma matsaya ba tsakanin ɓangarorin biyu dangane da dawo da tallafin man fetur ɗin da gwamnatin ta janye wanda ya janyo zanga zanga da yajin aiki na gama gari a ƙasar

https://p.dw.com/p/13jsg
Protesters hold placards and shout slogans on Ikorodu road in Nigeria's commercial capital Lagos January 3, 2012. Hundreds of demonstrators in Nigeria's commercial capital Lagos shut petrol stations, formed human barriers along motorways and hijacked buses on Tuesday in protest against the shock doubling of fuel prices after a government subsidy was removed. REUTERS/Akintunde Akinleye (NIGERIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST ENERGY)
Masu gudanar da zanga zanga akan tsadar man fetur a NajeriyaHoto: Reuters

An watse baram baram a tattaunar da aka yi tsakanin wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da na gwamnatin a ƙarƙashin jagorancin shugaba Gooluck Jonathan.Masu aiko da rahotannin sun ce an kasa cimma daidaito tsakanin sasan biyu akan maganar dawo da tallafin man feur ɗin da gwamnatin ta janye wanda ya hadasa tashin frashin man fetur a bisa kasuwanni .

Kuma nan gaba a wani lokacin da ba a tantance ba za a sake komawa kan tebrin shawarwarin.Yan ƙwadagon na son da a dawo da frashin lita ɗaya na man a naira 65 kamar yadda yake a da to amma kuma gwamnati ta ƙi amincewaMasu yin nazari akan al amuran yau da gobe na hasashen cewa a cikin ƙwanaki na gaba za a shiga cikin wani mawuyacin hali inda har aka kasa samun bakin zaran rikicin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal