1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Majalisa na nazarin matakin dage zabe

February 5, 2024

Majalisar dokokin kasar Senegal da fara zama a wannan Litinin domin yin nazari kan wani rahoto da ya ba da shawarar dage babban zaben kasar wanda tun da farko aka tsara gudanarwa a karshen watan Fabarairu.

https://p.dw.com/p/4c3kv
Majalisar dokokin Senegal
Senegal: Majalisa na nazarin matakin dage zabeHoto: Carmen Abd Ali/AFP/Getty Images

'Yan majalisa na bangaren dan takara Karim Wade wanda aka yi watsi da takarasa tare da goyon bayan 'yan bangaren shugaba mai barin gado Macky Sall ne suka shigar da wannan bukata ta a dage zaben da watanni shida ko kuma da shekara guda saboda wadansu dalilai da suka bayyana.

Karin bayani: AU ta nemi Senegal da ta gaggauta gudanar da babban zaben shugaban kasa

Ana dai bukatar samun amincewar kashi uku cikin biyar na 'yan majalisar dokokin su 165 kafin a aiwatar da wannan bukata da ta haifar da bore a kasar dake Yammacin Afrika.

Karin bayani: 'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal

A daidai lokacin da ake fara zama majalisar 'yan adawa sun kira zanga-zanga lamarin ya sa aka karfafa matakan tsaro tare da katse hanyar sadarwa ta intanet a birnin Dakar da ke zama fadar gwamnati.