1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance rikicin siyasar Senegal

Robert Adé RAM/LMJ
February 26, 2024

An fara taron tattaunawa kan siyasa da Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya shirya, domin magance rikicin siyasa da kasar ke fama da shi a Diamniadio da ke kusa da Dakar babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4cte8
Senegal | Zanga-Zanga | Adawa | Dage Zabe | Macky Sall
Shugaban kasar Senegal Macky SallHoto: DW/AFP

Sai dai 'yan takarar shugabancin kasa 16 da 'yan kungiyoyin farar hula da dama, sun ki halartar zaman da za a shafe kwanaki biyu ana yi. 'Yan takarar da ke cikin gungun "Aar Sunu" sun bayyana tattaunawar da Shugaba Macky Sall din ya shirya, a matsayin shirme. Alimou Barro wanda ya taimaka wajen kafa jam'iyyar Pastef da aka rusa da kuma ke goyon bayan dan takara Bassirou Diomaye Faye da har yanzu yake tsare a gidan yari, na da ra'ayin cewa sanar da jadawalin zaben shugaban kasa ya fi gudanar da zaman tattaunawa.

Senegal | Zanga-Zanga | Adawa | Dage Zabe | Macky Sall
Kungiyoyin fararen hula, na kan gaba wajen zanga-zanga kan dage zaben na SenegalHoto: John Wessels/AFP

Sai dai taron tattaunawar na da matukar muhimmanci a yanayin da ake ciki na rikice-rikicen siyasa da na hukumomin da suka dage zaben kasar, a cewar Mamadou Ndoye da ke zaman mamba na gungun kawancen jamhuriya APR kuma babban sakataren "Ngor Debout a diaspora". Wasu magoyin bayan hadin gwiwar Benno Bokk Yakaar da ke mulki na goyon bayan gudanar da taron tattaunawar, amma ba su amince da wadanda kotun tsarin mulki ba ta amince da takararsu ba su shiga taron. Sai dai a daidai lokacin da aka kaddamar da tattaunawar samar da maslahar siyasa a Senegal din, ana samun masu lashe amansu bayan nuna adawa ga taron.

Senegal | Dakar | Macky Sall | Siyasa | Zanga-Zanga
Zanga-zangar adawa da matakin Shugaba Macky Sall na SenegalHoto: John Wessels/AFP

#b#A wata hira da aka yi da dan takara Aly Ngouille Ndiaye mamba na gungun 'yan takarar shugaban kasa a wata kafar yada labarai a Dakar, ya tabbatar da cewa zai halarta. A wannan yanayi ne a karshen mako a birnin Dakar, wasu kungiyoyi biyu masu fafutuka suka gudanar da wani taron jerin gwano. Daya na masu adawa kan dage zaben shugaban kasa, dayan kuma na masu kawance da gwamnati a kan taron tattaunawar siyasar na kasa wadda za a sanya sabuwar ranar gudanar da shi.