1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: RSF za ta bude hanyar fita daga Darfur

May 18, 2024

Rundunar mayakan RSF da ke Sudan sun sanar da shirinsu na bude hanyoyin fita daga yankin El-Fasher da ke Darfur.

https://p.dw.com/p/4g1rE
Mayakan RSF na Sudan
Mayakan RSF na SudanHoto: Mohamed Babiker/Photoshot/picture alliance

Rundunar mayakan RSF ta ce za ta bude hanyoyin fita daga yankin El-Fasher da ke Darfur, sakamakon fadan da ya sake rincabewa a makwannin baya-bayan nan. A sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya, ta ce za ta taimaka wa jama'a su bar yankin zuwa wasu sassan kasar tare da ba su kariya.

Karin bayani: 

RSF ta bukaci mazauna El-Fasher da su kaurace wa yankunan da ake fada da ma inda za su iya kai wa farmaki. Fiye da shekara guda kenan da Sudan ta fada cikin rikicin shugabanci tsakanin shugaban rundur sojin kasar, Abdel Fattah al-Burhan da kuma na RSF da ke karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo. Rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 15,000 a cewar kwararru a Majalisar Dinkin Duniya.