1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 10,000 sun bace a Libiya

September 13, 2023

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tattara kayan agaji ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a mummunar ambaliyar ruwa da ta kashe dubban mutane a Libiya.

https://p.dw.com/p/4WGk6
Hoto: Jamal Alkomaty/AP Photo/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na aiki ne da kungiyoyin agaji na cikin gida da kuma na kasa da kasa domin kai daukin gaggawa ga wadanda ke yankunan da iftila'in ya shafa a Libiya. A yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.

Karin bayani: Guguwa da ambaliya sun kashe rayuka a Libiya

Kungiyoyin bayar da agaji sun ce,  ana neman wasu mutane kimanin dubu goma da suka bace sakamako mummunar guguwar ta Daniel. Ministan harkokin cikin gida na kasar ya tabbatar da mutuwar mutane fiye da 5,200.