1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar kere-kerea Kaduna

January 19, 2022

Matashin Musa Muhammad ya kware wajen aikin kere-kere wanda ta hanyarsa wasu matasan kan samun horo domin yin dogaro da kai.

https://p.dw.com/p/45lxN
Nigeria | HdM: Maiduguri Deco (M)
Hoto: Al-Amin Suleiman Muhammad/DW

Musa Muhammad Ibrahim Matashi  ne mai basira da kishin matasa, yana da wani katafaren wurin kere-kere, inda ake koyawa matasa design a manyan kofofi wato gate, da na masallatai, da duk wani abu da ke da bukatar design a jikinsa, kuma duk abin da ka zo da shi za a iya kera maka irin shi.Yana da yaran masu aiki matasa  30 a karkashinsa, an kuma yaye da dama wannan sana'a tana matukar rufa masa asiri.