1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta bai wa Ukraine tallafin dala biliyan 95

Abdul-raheem Hassan
February 13, 2024

Bayan zazzafar muhawa kan kudaden tallafi, a karshe majalisar dattawan Amirka ta samu rinjayen kuri'u 70 bisa 20 na amincewa da kudurin kudaden agaji dala biliyan 95 ga kasashen Ukraine da Isra'ila da kuma Taiwan.

https://p.dw.com/p/4cLqs
Joe Biden, shugaban kasar Amirka
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Duk da cewa kudurin ya samu sahalewar majalisar dattawa, amma babu tabbas kan makomar kudurin a zauren majalisar wakilai, inda tsohon Shugaban kasar Amirka Donald Trump kuma dan takaran shugaban kasa ya bukaci ‘yan jam’iyyar Republican da su guji zartar da dokar da za ta bai wa Shugaba Joe Biden damar samun nasara a majalisa.

Washington na daukar Ukraine a matsayin babbar kawa da ke bukatar agajin kare kai da kayan yaki daga barazanar mamar Rasha, gwamnatin Shugaba Bidenn ta kashe sama da dala biliyan 44 ga Kyiv tun bayan fara yakin a watan Febrairun 2022.