1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

LGBTQ+: Kurkukun Ghana ka iya fuskantar barazana

February 16, 2024

Dan majalisar Ghana ya bukaci zauren majalisar da ta sauya tunani kan tura masu neman jinsi daya gidan yari domin za su iya gurbata tunanin wadanda ke zaman wakafi, inda ya bukaci killacesu tare da shawarwari.

https://p.dw.com/p/4cVQR
Hoto: Isaac Kaledzi/DW

Dan majalisar Alexander Afenyo-Markin, ya ce dokar hukunta masu neman jinsa daya da ke kokarin tsallake karatu a zauren majalisar ba abin da zai harfar illa yaduwar neman jinsi daya a gidajen yarin kasar.

Karin Bayani: Limaman Kirista na ci gaba da saba wa yin tabarruki ga auren jinsi

Gamayyar kungiyoyin mabiya addinin Kirista da na Islama harma da sarakunan gargajiya na daga cikin wadanda suka bukaci gabatar da kudurin da galibin 'yan majalisar dokokin kasar ta Ghana suka amince da daurin shekaru har zuwa 10 ga masu neman jinsi.

Karin Bayani:

Matakin Yuganda ya janyo damuwa

An kai matakin karshe na tattaunawa kan kudurin da ake kokarin gabatar da ita a matsayin doka, da hakan ke ci gaba da jefa masu neman jinsi daya a Ghana cikin zullumi.