1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun dakatar da yajin aikin gama gari

January 16, 2012

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun janye yajin aiki bayan da gwamnati ta amince da rage farashen litar man fetur daga Naira 141 zuwa 97.

https://p.dw.com/p/13kTI
A cabbage cleaner stands in front of fuel trucks in Lagos, Nigeria, Sunday, Jan. 15, 2012. Nigeria's government and labor unions failed to end a paralyzing nationwide strike over the high costs of gasoline, and potentially sparking a national oil production shutdown. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: dapd

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sanar da janye yajin aikin gama gari da ta shiga, tare da amincewa da farashin Naira 97 a kan kowace litar man fetir da gwamnatin kasar ta sanar.

Sanar da janye yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriyar ta yi ,ya biyo bayan daukan lokaci mai tsawo da shugabanin gudanarwar kungiyar suka yi a Abuja, inda suka tattauna a game da mataki na gaba da ya kamata su dauka a kan wannan batu, musamman bayan jawabin da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya yi wa al'uma, inda ya sanar da amincewa da rage farashin litar mai daga Naira 141 da gwamnatin ta sanra zuwa naira 97.

Sanar da janye dakatar da yajin aikin dai na kunshe ne a sanarwar da shugaban  kungiyar kwadagon Najeriyar Comrade ya bayyana yana cewa:

Yace bisa ga abubuwa da ke faruwa ina sanar da dakatar da yajin aikin saboda dalilai da muka hango na iya sauya matakin da muka sanya a gaba.

Wannan mataki na kungiyar kwadagon Najeriyar ta dauka daya  biyo bayan dakatar da zanga zanga ya nuna cimma matsaya a kan yajin aikin da ya gurgunta harkokin tattalin arzikin Najeriya.

Demonstrators protest against the elimination of a popular fuel subsidy that has doubled the price of petrol in Nigeria's captial Abuja, January 10, 2012. Nigerians took to the streets on Tuesday in growing numbers on the second day of protests against a sharp increase in petrol prices, piling pressure on President Goodluck Jonathan to reverse his removal of fuel subsidies. REUTERS/Afolabi Sotunde (NIGERIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST ENERGY)
Hoto: dapd

Sakataren gudanarwa na kungiyar kwadagfon Najeriya Comrade Abbayo Nuhu Toro, ya bayyana dalilan da suka hango suka sanya su janye yajin aiki.

To sai dai sanin cewa an dade ana wa kungiyar kallon wace kan bari gwamnati ta yi amfani da ita a lokutan baya, da ma dagewar da ta yi  a baya a kan lallai sai an koma kan farashin Naira 65, abinda ya sanya tambayar Comrade Abbayo Nuhu Toro Abdulwaheed Omar, ko mi ya sa suka amince da wannan farashi.

Kafin kaiga daukan wannan mataki da gwamnati ta sasauto saida shugaban Najeriya ya yi taro da gwamnonin kasar a daren Lahadi, inda suka amincewa da sasautowa bayan da mummunan yajin aikin ya gurgunta harkoki a Najeriya tare da sanya gwamnati tafka mummunar asara.

Shugaban Najeriyar dai ya yi alkawarin ci gaba da buda harkar man fetir din don baiwa 'yan kasuwa ikon su ci gaba da shiga don a taka da su, abinda kai staye ke nufin ci gaba da bin batun janye tallafin man fetir a cikin kasar, to sai dai ga Dr Jibo Ibrahim, shugaban kungiyar bunkasa demokradiyya ta Najeriya, wadanda suka kasance kan gaba wajen  zanga zangar  nuna adawa da janye tallafi na mai ra'ayin cewa su ba haka suke kallon al'ammuran ba.

People protest following the removal of fuel subsidy by the Government in Lagos ,Nigeria, Monday, Jan. 9, 2012. Labor unions began a paralyzing national strike Monday in oil-rich Nigeria, angered by soaring fuel prices and decades of engrained government corruption in Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: dapd

Abin jira a gani shine ko sauran kungiyoyin kare hakin jama irin na masu yunkurin mammaye Najeriya zasu amince da matakin da kungiyar kwadagon kasar ta dauka da ma irin tasirin da hakan zai iya yi a wannan lamari, kasancewwa wannan shine yajin aiki mafi muni da aka fi daukan tsawon lokaci a tarihin Najeriyar, yajin aikin da ya hada kan al'ummar kasar tun bayan rigingimun zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta gabata.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss

Edita:Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani