1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas

May 20, 2024

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifukan kasa da kasa ICC ya bukaci sammacin cafke firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da shugabannin Hamas bisa zargin haddasa yakin Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4g4i8
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaiministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Maya Alleruzzo/AP/dpa/picture alliance

Karim Khan ya ce ICC na kuma bukatar kama ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da shugabannin Hamas uku da suka hada da Yehya Sinwar da Mohammed Deif da kuma Ismail Haniyeh, bisa zarginsu da hannu wajen mutuwar dubban mutane da keta hakkin bil adama da kuma rashin nuna jinkai kan al'ummar Zirin Gaza.

Karin bayani: ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne 

Khan ya ce ICC na da tarin hujjoji kan yadda dukkan bangarorin sukayi amfani da  'yunwa da kishirwa wajen azabtar da al'ummar Zirin Gaza wanda hakan ya sake jefa rayuwar mata da kananan yara cikin garari da ya yi ajalin mutane da dama.