1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kotun soji ta saki dan Bazoum Salem

Abdourahamane Hassane
January 9, 2024

Hukumomin mulkin soji a Nijar sun saki Salem Bazoum dan tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum wanda aka hambarar da gwamnatinsa a watan Yulin da ya gabata, wanda ake tsare da shi tare da mahaifansa.

https://p.dw.com/p/4b0Xt
Hoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

 A cewar wani hukunci da kotun sojan  Yamai ta yanke wanda kamfanin dillancin labaran na Faransa AFP ya bayyana ya ce Salem an yi masa sakin wucin gadi daga alkalin da ke bincike na kotun soji. Sannan kotun ta ce ya kasance cikin shiri idan shari'a na bukatarsa. Salem Bazoum, mai shekaru 23, ya bar Yamai zuwa Lomé.Togo dai ta kwashe makonni da dama tana ta yin tattaki domin shiga tsakani da gwamnatin sojan da ke kan madafun iko.