1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kayan karatun yara masu lalurar ido sun yi karanci a Afirka

January 4, 2024

Ilimin yaran da ke da larurar gani a na fuskantar matsala a Najeriya sakamakon tsadar kayayyakin Karatunsu, kasancewar daga ketare ne ake kawo su, Amma UNESCO ta kebe 04 ga watan Janairu don nazarin matsayin rubutun su.

https://p.dw.com/p/4arDL
Internationaler Tag der Menschen mit Behinderung
Hoto: China Photos/Getty Images

A wani sabon binciken da kungiyar kare hakkin masu bukata ta musanman a Afrika mai suna "Beyound the border of disabilty" ta gudanar, ta bayyana karara cewar tsadar na'urar da ke tallafa wa katatun 'masu larurar ido (Braille machine) na dakushe masu gwiwa wajen neman ilmi. Rilwanu Abdullahi, shugaban wannan kungiya ya bayyana cewar akwai matsoli da dama da ke shafar ilmin yara da ke da matsalar idanu a kasashen Afrika, inda talauci ya kasance daga cikin manyan kalubalen da ke haddasa iyaye gazawa wajen biya wa 'ya'yansu  kudaden karatu da kayayyakin karatu.

Karin bayani: Tunawa da ranar mutane masu bukata ta musamman

Salon rubuta da masu lalurar idanu ke yi da na'ura tsa musamman
Salon rubuta da masu lalurar idanu ke yi da na'ura tsa musammanHoto: Solomon Muche/DW

Rilwanu ya ce tsadar kayayyakin karatun yaran da ke da lalurar gani ya fi kowane bangaren ilimin yara a kasashen.Afrika sakamakon yadda rayuwa ta sanya wasu iyaye barin 'ya'yansu akan titi da kokon bara. Ya ci gaba da cewar, ana sayar da Na'urar karatu a kan Naira 250 000. Saboda haka ne suke yin kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a kan tallafa wa wadannan yara don ceto rayuwarsu daga duhun jahilci.

Karin bayani: Neman mafita kan tabarbacewar ilimin yara

An samar da jarida ta masu larurar idanu a Habasha
An samar da jarida ta masu larurar idanu a HabashaHoto: Solomon Muche/DW

Sauran kayayyakin karatun sun hada da allon karatu da alkalami, wanda su ma farashin ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da duniya ke bikin 04 ga watan Janairu a matsayin ranar tunawa da  na'urar da ke taimakawa masu larurar gani wajen karatu da sauran hanyoyin neman ilmin zamani.