1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karin kudi ga daliban jami'a

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 3, 2022

Majalisar dattawan Najeriya ta saka baki a kan rikicin da ya taso na karin kudin makaranta da aka yi a jami'o’i da manyan makarantun kasar.

https://p.dw.com/p/46U8q
Najeriya | Jami'ar Abuja
Jami'ar AbujaHoto: Universität Abuja

Daukacin jami'o'i da manyan makarantun Najeriyar ne dai suka yi karin kudin, inda wasu makarantun suka kara abin da ya kai sama da kaso 100. Matakin karin kudin makarantun ya tunzura dalibai, inda suka bayyana cewa suna shirin gudanar da zanga-zanga a kasar domin nuna rashin yardarsu. Daliban jami'o'in dai sun nuna takaicinsu kan karin kudin da suka ce ya zo a lokacin da su da iyayensu ke cikin mawuyacin hali, sakamakon matsalolin koma bayan tattalin arziki. Majalisar dattawan Najeriyar dai ta shiga lamarin, a kokarin kaucewa shiga zanga-zangar da dalibana suka tsara domin nuna kin amincewarsu. Wakilan daliban dai, sun gana da shugabannin majalisar dattawan Najeriyar a Abuja.
Duk da cika alkwari da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi  na karin kaso 50 cikin 100 na abin da ya kebewa ilimi a kasafin 2022, har yanzu Najeriyar ba ta kai adadin kaso 15 zuwa 20 da Hukumar Kula da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kasashe su kebe ba. Ana dai wannan tirka-tirka ne, a daidai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta gaza cikawa malaman jami'o'in alkawarin da ta yi musu na kudin gudanar da jami'o'in da ma alawus-alawus dinsu. Harkar ilimin boko a Najeriya dai ta dade tana cikin mawuyacin hali na rashin isassun kayan aiki da kudin gudanarwa, a daidai lokacin da ake kirkiro karin makarantun da wasu ke zama tamkar kango.

Najeriya | Majalisar Dattawa
'Yan majalisar dattawan Najeriya, sun magantu kan karin kudi ga dalibaiHoto: Uwais Abubakar Idris/DW