1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gomman mutane sun rasu a kifewar jirgin ruwa a Djibouti

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2024

Iftila'i a hanyar da dubban 'yan gudun hijira ke bi daga yankin kahon Afirka zuwa kasashen tekun fasha

https://p.dw.com/p/4f6hQ
Mutane da dama sun mutu a hadarin jirgin ruwa a Djibouti
Mutane da dama sun mutu a hadarin jirgin ruwa a DjiboutiHoto: International Organization for Migration/AP/picture alliance

Akalla mutane 16 suka rasu bayan da jirgin ruwan da suke ciki da ya taso daga Yemen ya kife a gabar kogin Djibouti a cewar kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya.

A wani jawabi da ta wallafa a shafin X da aka fi sani da Twitter a da, kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM ta ce jirgin na dauke da 'yan gudun hijira 77 yawancinsu kananan yara, inda ta kara da cewa akwai wasu mutanen 28 wadanda har yanzu ba a gano su ba.

Yawancin mutanen 'yan gudun hijirar Habasha ne da suka taso daga Yemen.

Jakadan Habasha a Djibouti Berhanu Tsegaye ya wallafa a twitter cewa mutane 33 ne suka tsira a hadarin. Hukumomin yankin na taimaka wa kungiyar kula da kaurar jama'a a cigaba da aikin ceto.

Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM ta ce a kowace shekara dubban 'yan gudun hijira daga yankin kahon Afirka musamman kasashen Habasha da Somalia suna barin nahiyar inda suke bi ta Djibouti da fatan samun aiki a Saudiyya ko kasashen yankin tekun Fasha.