1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Dabi'ar sace-sacen mutane na kara kamari a Najeriya

March 19, 2024

Akalla sau takwas ne satar mutane ta faru a cikin wata guda a Najeriya, lamarin da ya shafi sama da mutane 450 duk da sabbin fasahohin zamani da gwamnati da kuma jami'an ke amfani da su wajen magance matsalar tsaro.

https://p.dw.com/p/4dtqn
Iyaye na neman gwamnati ta ceto 'ya'yansu da a sace a makaranta
Iyaye na neman gwamnati ta ceto 'ya'yansu da a sace a makarantaHoto: Audu Ali Marte/AFP

Mutane kusan 500 ne aka sace bayan kashe da daman gaske a wani abin da ke kara fito da irin girman matsalar rashin tsaron da ke aadbar makarantun tarayyar Najeriya. Duk da cewar shekarar 2024 na kan gaba wajen samar da kudi domin kalubalantar annobar rashin tsaro, amma kasar na hangen ta'azzarar rashin tsaron a ko'ina. Abdul Aziz Sulaiman da ke zaman kakakin kungiyar dattawan arewacin Najeriya  ta Northern elders, ya ce babu gaskiya a bangaren 'yan mulkin bisa batun tsare rayukan al'ummar Arewa.

Kokarin sauke bashi ko neman mafitar rashin tsaro?

Yahuza Getso ya ce satar mutane ta zama kasuwanci mai riba a Najeriya
Yahuza Getso ya ce satar mutane ta zama kasuwanci mai riba a NajeriyaHoto: DW

Naira Triliyan uku ne ko kuma kaso 13% na daukacin kasafin kudin bana ne aka ware dominkokarin magance rashin tsaro da ke zama annoba ta kan gaba cikin Najeriya. Ko bayan mika daukacin mukamai na tsaron bisa shugabannin da cibiyarsu ke a Arewa, amma an kare a ta'azzarar annobar satar 'yan kasa a Kaduna da mafi yawan sassa na Arewa. Dr Yahuza Getso da ke sharhi kan rashin tsaron ya ce karuwar sace 'yan kasar don neman kudin fansa na zaman alamun zafi a bangaren barayin da ke kara fuskantar hari na jami'an tsaro.

Ana wasan buya tsakanin jami'an tsaro da barayin daji

'Yan makaranta na cikin wadanda ak fi sacewa a yankin arewacin Najeriya
'Yan makaranta na cikin wadanda ak fi sacewa a yankin arewacin NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Akalla jihohi 19 na tarayyar Najeriya ne ya zuwa yanzu ke fama dafargabar tsaro musamman annobar sace mutane a cikin kasar da kuma ke kallon rikicin cin hanci a matakan mulki da dama. Arewacin tarrayar Najeriyar na shirin kallon karin rikici baya ga batun karuwar talauci, a cewar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan batun harkokin mulki na tarayyar Najeriya.