1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya za ta tura 'yan gudun hijira zuwa Ruwanda

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2024

Gwamnatin Burtaniya ta sanar da fara tsare 'yan gudun hijira da suka shiga kasar inda cikin 'yan kwanaki za ta tura su zuwa Rwanda bayan samun amincewar majalisar dokoki ,

https://p.dw.com/p/4f6LT
Jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira
Jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijiraHoto: Gareth Fuller/PA/AP/picture alliance

Matakin gwamnatin ya jawo kakkausar martani daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Firaministan Burtaniyar Rishi Sunak ya ce ba gudu ba ja da baya game da wannan matakin da suka dauka wanda ya ce zai dakile kwararar bakin haure zuwa cikin kasar.

Rishi Sunak ya ce jirgin farko zai tashi daga Burtaniya zuwa Ruwanda cikin makonni 10 zuwa 12 masu  zuwa

Karin Bayani: Burtaniya ta kafe kan bakanta na aikewa da 'yan gudun hijirar cikin kasar zuwa Rwanda

A karkashin yarjejeniyar 'yan gudun hijirar da suka Burtaniya ta barauniyar hanya za a tura su Ruwanda inda za a tantance bukatarsu ta neman mafaka, idan an amince to za a iya barinsu su zauna a Ruwanda.

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya yi kira ga Burtaniya ta sake nazarin matakin da ta dauka  wanda ya ce ya saba da dokar kare hakkin dan Adam

Karin  Bayani: Ruwanda: Ayarin 'yan cirani ya sauka a Kigali

A waje guda 'yan sa'oi bayan da majalisar dokokin Burtaniyar ta amince da matakin gwamnatin, wani jirgin ruwa dauke da yan gudun hijira  112 yawancinsu yan Syria da 'yan Iraqi ya sa sami matsala inda fasinjojin suka rika fadawa kogi da ke da tsananin sanyi.

A kalla mutane biyar suka mutu da suka hada da wata yarinya 'yar shekara bakwai da maza uku da kuma wata mace guda.