1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFCON: Côte d'Ivoire ta ciri Tuta

Mouhamadou Awal Balarabe
February 12, 2024

Côte d'Ivoire ta zama zakaran da Allah ya nufa da cara a gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka, lamarin da ya bakanta zukantan magoya bayan abokiyar karawarta ta Najeriya.

https://p.dw.com/p/4cJtV
AFCON Finale
Hoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance/dpa

Da kyar na tsira ya fi da kyar aka kama ni wannan shi ne abin da ya faru ga Côte d' Ivoire da dan wasanta Frank Kessie ya yi nasarar farke kwallon da William Troost Ekong na Najeriya ya zura a minti 38 da fara wasan karshe na cin kofin Afcon. Daga bisani ma dai, dan kwallon Borussia Dortmund Sebastien Haller ya raba gardama mintuna 9 kafin a tashi wasa inda ya ci wa kungiyarsa ta Les elephants kwallon na biyu kuma na karshe. Wannan dai ya bai wa Côte d'Ivoire damar samun Kofinta na 3 baya ga na 1992 da kuma 2015. Sai dai a wannan karon, dan gari ne ya ci gari saboda karkashin horaswar dan gida Faé Emerse da ya taba buga wa Côte d'Ivoire kwallo a baya hakarta ta cimma ruwa. Ga ma abin da koci Faé ke cewa bayan wannan nasara

'Yan kungiyar kwallon kafa ta Cote d'Ivoire, zakarun AFCON
'Yan kungiyar kwallon kafa ta Cote d'Ivoire, zakarun AFCONHoto: FRANCK FIFE/AFP

"Wannan ya fi karfin tatsuniya, har yanzu ina tantamar cewar mun kai labari duba da irin kalubale da mummunan yanayin da muka samu kanmu a ciki a wannan gasa, musamman lokutan da ake binmu kwallo kuma muke farkewa daga bisani, yana da ban mamaki, wani abin al'ajabi ne. Mun yi iya kokarinmu don lashe wannan kofi, gwiwarmu ba ta taba mutuwa ba, mun nuna cewar mu maza ne, kuma mun iya juriya duk da wahalar da muka sha."

Côte d' Ivoira ta zama kasar farko da ta lashe kofin kwallon kafar Afirka da ta shirya a cikin shekaru 18 da suka gabata, inda Masar ta kasance ta karshe a 2006. Abin da ya fi bada mamaki ma dai, shi ne yadda Côte d' Ivoire ta tashi daga wacce kiris ya hana a yi waje road da ita a  wasan rukuni i zuwa wacce ta lashe kofin bana, lamarin da ya sa 'yan kasar nuna farin cikinsu.

Mazauna Abidjan da sauran garuruwa na Côte d' Ivoire sun kwana suna kade-kade da raye-raye tare da nuna godiya ga wadanda suka taimaka wajen ci musu kofin Afirka.

Wani mai goyon bayan kungiyar Cote d' Ivoire
Wani mai goyon bayan kungiyar Cote d' IvoireHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Wannan na cewa" Wannan ya zarta tunanina, ba zan iya bayyana abin da nake ji ba. Amma na yi imanin cewar za mu iya lashe wannan kofi, kuma na ci gaba da samun kwarin gwiwa har karshe."

A nata bangaren, Super Eagles ta Najeriya ta sa ran lashe kofin saboda gogaggun 'yan wasa da take da su irin su Esimhen da sauransu. Sannnan rabon ta buga wasan karshen tun 2013. Saboda haka ne wasu 'yan Najeriya suka bayyana wa wakilinmu na kaduna Mohd Mohd bacin ransu

To baya ga Côte d' Ivoire da ta lashe kofin da kuma Najeriya a matsayi na biyu,  Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu ta ya nasara darewa matsayi na uku bayan da ta doke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a bugun fenariti. Maroko ce za ta dauki bakunci gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka a watanin Yuni da Yulin 2025.

Yanzu kuma sai fagen Bundesliga, inda aka gudanar da wasannin mako na 21 na babban lig din kwallon kafar Jamus a karshen mako. Kuma nasarar da Bayer Leverkusen ta samu da ci 3-0 a karon batta da ta yi da Yaya-babba Bayern Munich ta ba ta damar yi wa kowa rata a saman teburi da maki 55, yayin da kungiyar Munich ke biye mata baya da maki 50. Godiya ta tabbata ga 'yan wasan Josip Stanisic da Alex Grimaldo da Jeremie Frimpong da suka zura kwallo, lamarin da ya sa kocinsu Xabi Alonso na Bayer Leverkusen nuna doki da murna.

Bundesliga: Karawar Bayer Leverkusen da Bayern München
Bundesliga: Karawar Bayer Leverkusen da Bayern MünchenHoto: Martin Meissner/AP Photo/üicture alliance

" wasan yau ya dan bambanta da sauran wasannin kakar wasa. Ba mu samu damar rike kwallo a mafi yawan lokuta ba, amma kasancewa mun iya sajewa da irin wannan yanayi kuma muka ci gaba da kalubalantar kungiya kamar Bayern , yana nufin cewa kwazon kungiyarmu na habaka, ma'ana a shirye take ta buga wasanni masu wahala ba tare da rugujewa ba."

A bangaren Bayern Munich, wannan rashin nasara ya yi matukar illa ga kwarjininta, saboda a yanzu ratar maki biyar ne ke raba ta da abokiyar hamayyarta Leverkusen, sannan 'yan wasan da Thomas Tuchel ke horaswa sun kasa girgiza abokin karawar su, lamarin da Harry Kane ya ce abin takaici ne.

"Ba mu taka rawar gani ba alhali muke rike da kwallo. Ba mu matsa musu lamba sosai ba, amma duk lokacin da muka samu kwallon mun rinka mayar da ita kai tsaye,  kuma hakan ya ba su damar samun karfin gwiwa a wannan wasan. A mintunan karshe ma, ba mu yi wasa mai kyau ba lokacin da muka kai hari ga masu tsaron bayan ba. Don haka rana ce mai ban takaici sosai saboda mun samu damarmaki da yawa."

Baya ga  Bayer Leverkusen da Bayern Munich da ke a matsayi na daya da na biyu, ita ma Stuttgart tana ci gaba da mannewa a matsayinta na uku da maki 43 bayan da ta doke Mainz da ci 3-1. Ita kuwa Yaya-karama Borussia Dortmund ta lallasa Freiburg da ci 3-0. A sauran wasannin kuwa, Augsburg da Leipzig sun tashi 2-2, yayin da  Union Berlin ta samu muhimmiyar nasara a  Wolfsburg da ci 1-0. Don haka 'yan Berlin na gaban Cologne da ke a matsayi na 16 bayan da suka tashi 1-1 da Hoffenheim. A daya bangaren kuwa, Frankfurt da Bochum sun yi kunnen doki 1-1, yayin da 'yar auta Heidenheim ta bi Werder Bremen har gida kuma ta doke ta da ci 2-1. Sannan an yi canjaras tsakanin Mönchengladbch da Darmstadt 0-0.

Kiptum dan gudun fanfalaki ya rasu
Kiptum dan gudun fanfalaki ya rasuHoto: Eileen T. Meslar/Chicago Tribune/AP/dpa/picture alliance

A wani batu mai ban tausayi kuwa, mai rike da kambun gudun fanfalaki na duniya Kelvin Kiptum na Kenya ya mutu a wani hatsarin mota a yammacin wannan kasa a ranar lahadi da maraice yana da shekaru 24 da haihuwa. Kafofin yada labaran kasar Kenya da dama sun bayyana cewar, matashin da ya fi kowa gudu a tsawon kilomita 42 a duniya ya gamu da ajalinsa ne kan hanyar zuwa garin Eldoret bayan horo da ya samu a Rift Valley da ya shahara a fannin tseren nisan zango a Kenya.

Shi ma kocinsa Gervais Hakizimana na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari, yayin da wata mace da ta ji rauni take asibiti a halin yanzu.

Tuni dai shugaban hukumar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya Sebastian Coe ya bayyana alhinin rashin dan tsere Kelvin Kiptum a cikin wata sanarwa, yayin da David Rudisha dan kenya da ya lashe  tseren mita 800 na duniya sau biyu ya aika dai sakon nuna kaduwa da bakin ciki da abin da ya kira "babban rashi" a dandalin sada zumunta na X.

Mutuwar ta zo ne a kwanaki kalilan bayan da dan tsaren na kasar Kenya Kevin Kiptum ya sanar da cewa zai yi kokarin zama mutum na farko da zai yi gudun fanfalaki a hukumance a kasa da sa'o'i biyu a Rotterdam a ranar 14 ga watan Afrilu mai zuwa. Dama dai ya lashe gudun fanfalaki na London a shekarar 2023 a lokacin da yake kan ganiyar kuruciyarsa, wanda ba kasafai ake samunsa ba a gudun fanfalaki, wanda kwararrun 'yan tsere kuma shekaru suka fara turawa suka saba lashewa.