1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanene Desmond Tutu

Bashir, AbbaJanuary 28, 2008

Taƙaitaccen tarihin Desmond Tutu

https://p.dw.com/p/Cyux
Archbishop Desmond TutuHoto: AP Photo

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.



Tambaya: Don Allah filin amsoshin takardunku, ku ba ni tarihin Desmond Tutu, kuma waɗanne irin abubuwa ya yi har sunansa ya bazu a duniya. Ni ne mai saurarenku yau da kullum Mathew Auta, Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya.


Shi dai Desmond Tutu, an haife shi ne a shekarar 1931, a wani gari mai arziƙin Zinari da ake kira Transvaal, dake ƙasar Afirka ta kudu. Desmond Tutu ya ɗauko hanyar mahaifinsa ta aikin malanta, to amma a bisani ya dakata da aikin mallantar a lokacin da aka ɓullo da dokar tafiyar da ilimi da aka yi wa laƙabi da “Bantu Education Act” a shekarar 1953. Don haka ne sai ya shiga aikin bushara a majami'u, a inda ya sami matuƙar goyon baya daga Turawan dake aikin bushara a wancan zamani, musamman ma goyon bayan da ya samu daga Bishop Trevor Huddleston, sakamakon yadda ya nuna ƙiyayya ga wariyar launin fata.


Desmond Tutu shi ne ya kasance babban limamin ɗarikar Angilika na farko baƙar fata a birnin Johannesburg, dake ƙasar Afirka ta kudu, a shekarar 1975. Bayan shekara guda da kasancewa a wannan matsayi ne sai shugabannin Turawa fararen fata suka soma sa misa ido saboda irin ƙyamar da yake ga wariyar launin fata, don haka ne ma ya zamanto mai fafutikar yaƙi da mulkin wariyar launin fata. A lokacin da tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela ke zaman fursuna, Archbishop Desmond Tutu ne ya zamanto babban mai riƙe wuya ga ‘yan mulkin wariya, don haka ne ma ya sami wata lambar yabo a shekarar 1984, sakamakon wannan gwagwarmaya tasa a wancan zamani.


Yayin da Nelson Mandela ya fita daga gidan fursuna, an kafa hukumar sasantawa da bincike kan irin ta'annati da aka gudanar lokacin mulki wariyar launin fata a Afirka ta kudu, an naɗa Desmond Tutu ne shugaban hukumar. To amma kafin lokacin, a shekarar 1986, an zaɓe shi a matsayin babban Arch Bishop na birnin Cape Town, domin ya ci gaba da yaƙi da manufofin wariyar launin fata. A watan Maris, na 1988, Arch Bishop Desmond Tutu, ya fito fili don bayyana adawarsa ga ‘yan mulkin wariya, don haka sai ya ci gaba da yin kanfe ga jama'a da su ƙauracewa babban zaɓen lardi da gwamnatin shuagaba F W De Klerk ta shirya yi.


A lokacin da Nelson mandela ya naɗa Desmond Tutu shugaban hukumar binciken gaskiya da sassantawa na Afrika ta kudu, ya yi ƙoƙarin tattaro bayanai daga jama'a daban-daban da suka bayar da bahasi gaban hukumar, to sai dai kuma a yayin da yake aikin binciken ya kamu da wani ciwon daji, to amma duk da hakan a ƙarshen rahotonsa, Desmond Tutu ya zargi akasarin shugabannin da suka yi mulki a lokacin Turawan mulkin mallaka cewar ba su bayar da bahasi na gaskiya ba a gaban hukumar, musamman ma yadda baƙaƙen fata ke nunawa a zahiri irin cin zarafin da suka fuskanta a zamamin mulkin wariya a duk lokacin da suka je bada nasu bahasin.


Arch Bishop Desmond Tutu ya zamanto masani ne kan harkokin yau da kullum da kuma siyasar duniya, don haka nema wani lokaci a shekara ta 2002, ya zargi ƙasar Israila da tafiyar da manufofin mulki irin na wariya, sakamakon yadda take gallazawa al'ummar Falasɗinawa. Hazalika a shekarar ta 2002, Desmond Tutu ya gargaɗi Shugaba Robert Mugabe na ƙasar Zimbabuwe cewar kada ya riƙa tafiyar da mulki irin na kama- karya kan al'umma ‘yan ƙasar Zimbabuwe. Irin wannan fadakarwa ta Desmond Tutu ba ta bar shugabanin ƙasashen yamma ba, don kuwa Desmond Tutu ya buƙaci Shugaba George Bush na Amirka, tare da Firaministan Birtaniya Toni Blair, da su fito su gayawa duniya sun yi kuskure sakamakon yadda suka ƙaddamar da yaƙi kan ƙasar Iraqi, yaƙin da har yanzu babu wanda ya san ranar ƙarshensa sai Allah.