1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin Kirismetti tsakanin al´umomi daban daban a Bonn

December 20, 2007

Kowa da kowa na shiga cikin bukukuwan na Kirismetti a Jamus

https://p.dw.com/p/CeFz
Fitilu a ko ina a lokacin Kirismetti a JamusHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Ga al´umar Jamusawa lokuta gabanin ƙirismetti da kuma bukin kansa a cikin watan Disamba na zaman wani lokaci mai ƙayatarwa a shekara. A watan Disamban wannan shekara ba Kiristoci kaɗai ne ke wani buki na addini ba a´a sauran mabiya addinai daban daban na gudanar da nasu bukukuwan wato kamar musulmi dake bukukuwan babbar salla a wannan mako. Yayin da mabiya addinin Hindu suka gudanar da nasu bukukuwan cikin watan da ya gabata su kuma Yudawa a cikin wannan wata suke bukin Chanukka da ake yiwa laƙabi da bukin fitulu. Wato buki kan buki ke nan a cikin wannan wata na Disamba. To sai dai a daidai lokacin da ake gudanar da waɗannan bukukuwa tambayar da ake yi ita ce shin ko mabiya addinan daban daban suna haɗa kai don gudanar da waɗannan bukukuwa tare da wani birni mai cike da al´adu kamar na Bonn? Muna ɗauke da karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni Mohammad Nasiru Awal zan gabatar.

A duk inda ka zagaya a tsakiyar birnin Bonn zaka tarar da an ƙawata tituna da shaguna a wannan lokaci na shirye-shiryen bukin ƙirsimetti. Fituli da sauran kaya masu ƙyalli da wakoki irin na kirismetti sune abubuwan da suka mamaye harkokin yau da kullum a wannan lokaci gabanin bukin ƙirismetti. Kasuwanni na baje kolin kayan kirismetti kuwa a cike suke da jama´a. A gefen daya daga cikin waɗannan kasuwannin na kirismetti, Rashid Butt ya kafa wata rumfa ta tafi da gidanka inda yake sayar da zobba, sarƙar wuya da ´yan kunne. Rashid dai musulmi ne daga ƙasar Pakistan, kuma tun shekaru takwas da suka wuce yake nan Jamus. Ya ce buki ƙirismetti ba na shi ba ne duk da cewa yana sha´awarsa domin a kowane jajibiren ranar kirismetti Rashid ya na karɓar baƙoncin abokin sa Kirista.

Rashid:

Ya ce “Babban amini na Bajamushe ne. Kuma ni kaɗai ne abokinsa saboda haka ya ke zuwa gidana a wannan rana. Ya kan zo da kek sannan daga nan muna garzayawa gidan danginsa inda muke cin kek ɗin da abinci da sauran abin da ba a rasa ba. Wato mu biyu ne musulmi sauran kuma kiristoci amma dukkanmu muna wannan buki tare.”

Rumfar Rashid dai ba ta da tagar baje kolin kayan da yake sayarwa. Saboda haka bai ƙawata rumfar da wasu kaya masu kyalli na kamar yadda yake bisa al´ada a nan Jamus ba. Maimakon haka sai yana rage farashin kayansa don jawo hankalin mutane.

Rashid:

“Ina ƙoƙarin rage farashin kayana musamman ga masu sayen kayan kyaututtuka, domin sun fi son a yi musu rahusa.”

Kiristocin dai na jin daɗin haka domin kayan kyaututtuka wani ɓangare ne na bukin Kirismetti.

´Yan mitoci kadan da rumfar ta Rashid abubuwa sun banbanta. A gamaiyar Yahudawa ta birnin Bonn yara ne ke rera wakoki na bukin Chanukka na Yahudawa wanda kamar Kirismetti shi ma ake gudanarwa a cikin watan Disamba. Daga cikin wadannan yaran kuwa ´ya´yan Kirstin Silbernik, ´yar Katholika amma minjinta Bayahude. Suna gudanar da bukukuwan guda biyu. Gabanin Kirismetti yaran na gwajin wakoƙin na bukin Chanukka a wurin ibadar Yahudawan sannan daga baya su garzaya kasuwar Kirismetti.

Silbernik:

“Ko shakka babu muna ƙawata wannan wuri muna kunna kyandir kuma muna sanya sabbin kaya masu kyau. To sai dai ba ma zuwa coci, a nan wurin ibadar Yahudawa muke bukin kirismetti. Muna bawa yaran mu kyaututtuka, rabi saboda Kirismetti rabi kuma saboda bukin Chanukka.”

Ko da yake bukin Chanukka na matsayin wani muhimmin buki na iyali ga Silbernik mai bin addinin Kirista, amma har wayau Kirismetti na zaman wani buki na musamman a gare ta.

Silbernik:

“A gareni bukin Kirismetti ya fi na Chanukka ban sha´awa, musamman idan aka gayyace mutum zuwa wani wuri da aka kawata shi da bishiyar ƙirismetti da abubuwa masu ƙyalli. Hakan yana burge ni ƙwarai da gaske. A lokacin Kirismetti na fi sa kaya irin na masu shagulgula fiye da a lokacin Chanukka.”

A nan Jamus ranar 24 ga watan Disamba ce ƙololuwar bukin Kirismetti, inda ´yan´uwa da sauran dangi ke haɗuwa a gida don gudanar bukin. Ba dai Kiristoci kaɗai ke wannan buki ba, kamar yadda iyalin gidan Shikapuri ´yan asalin ƙasar Indiya su ma suke taruwa a wannan yammaci na ranar 24 ga watan Disamba. To sai dai ba sa ajiye bishiyar Kirismetti a gidansu.

Tun kimanin shekaru 15 Madan Shikapuri wanda ɗan Hindu ne yake zaune a nan Jamus. Shi ma ya ƙawata rumfarsa don jawo hankalin abokannen cinikinsa wadanda kiristoci ne.

Shikupuri:

“Duk inda ka bi zaka ga an ƙawata tituna da fitulu masu launi daban daban sai ka ce kana cikin gidan rawa ne wato disco. Kana ganin baki su ma suna shiga cikin wannan hada-hada ta bukin Kirismetti, amma gaskiya ni ba na sanya fitulu. Jamusawa ba sa jin daɗin haka.”