1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya da kama mulkin Obama

January 20, 2010

Yau ne ake cika shekara daya da kama mulkin Obama a kasar Amirka

https://p.dw.com/p/LbzW
Shekara daya da Bush ya danka wa Obama ragamar mulkin AmirkaHoto: AP

A cikin watan janairun shekara ta 2008 ne Barack Obama ya kama aikinsa a fadar mulki ta White House bayan lashe zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2007, inda ya riƙa yayata cewar: I zamu iya, wato "Yes we can" da turanci a yaƙinsa na neman zaɓe. To sai dai kuma kimanin shekara ɗaya bayan kama ragamar mulkin an tabbatar cewa hatta mutum kamar Obama, wanda aka saka dogon buri game da shi, ba zai iya warware dukkan matsalolin da duniya ke fama da su ba.

An dai sha kwatanta Obama da tsofon shugaban Amirka John F. Keneddy ko Martin Luther Kung ko kuma Abraham Lincoln. A lokacin da ya kawo ziyara Berlin dubban dubatar mutane suka hallara domin yi masa maraba kuma a cikin ƙiftawa da Bisimilla aka sayar da littafin tarihin rayuwarsa a dukkan sassa na duniya. To sai dai kuma ba a daɗe ba murna ta fara komawa ciki dangane da sabon shugaban na Amirka. Ga ba ɗaya dai duniya ta sa ran cewar Obama zai kawo canji ga manufofin ƙetare na magabacinsa Gerge W. Bush a cikin gaggawa, a yayinda su kuma Amirkawa suka yi fatan cewar sabon shugaban zai mayar da hankalinsa ne kacokam akan manufofin na cikin gida ta la'akari da matsalar taɓarɓarewar al'amuran tattalin arziƙin da ta kunno kai. Cimma waɗannan manufofin guda biyu a lokaci guda abu ne mai wuya, hatta ga jami'in siyasa mai hazaƙa irin Barack Obama. Bisa ta bakin Reinhard Rode ƙwararren masani akan al'amuran Amirka a jami'ar Halle dake gabacin Jamus, tauraruwar Obama ta ɗan dusashe a cikin watanni 12 da suka wuce.

"Galibi dai ya samu goyan baya ne daga ƙasashen Turai da kuma wasu Amirkawa da suka juya wa magabacinsa baya sakamakon ƙosawar da suka yi da manufofinsa, inda aka kusa a mayar da shi tamkar wani bawan Allah ne a al'amuran siyasa. A irin wannan hali ba shakka sannu a hankali murna tana iya komawa ciki bayan tafiya-tayi-tafiya."

Binciken ra'ayin jama'a da aka gudanar a Amirka ya nuna cewar an samu koma baya dangane da magoya bayan Obama lokacin da ya kama aiki a fadar mulki ta White House daga kashi 70 zuwa kashi 50 cikin ɗari. A nan nahiyar Turai kuwa ba dukkan matakansa ne ake marhaban lale da shi ba, saboda su ma Turawan tuni murnarsu ta koma ciki a game da dogon burin da suka saka na cewar Obama zai iya yin gaban kansa wajen shawo kan dukkan matsaloli na ƙasa da ƙasa da ake fama da su a cikin ƙiftawa da Bisimilla, kamar yadda aka ji daga bakin Michael Zürn, daga cibiyar nazarin kimiyya dake Berlin.

"Ba a cimma da yawa daga cikin abubuwan da aka yi fata ba. Wannan lamari ne da babu tababa akai. Babu wani takamaiman matakin da aka ɗauka dangane da al'amuran kasuwannin kuɗi. Kazalika ba a da wani takamaiman mataki dangane da kare kewayen ɗan-Adam a baya ga matsaloli daban-daban kamar rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya, wanda ba wani ci gaban da aka samu game da shi."

To sai dai kuma ko da yake babu wata gagarumar nasarar da shugaba Obama zai yi tinƙahon cimmawa a manufofi na ƙetare, amma ya kawo canjin alƙibla idan aka kwatanta da magabacinsa George W. Bush. Da farko dai ya dakatar da salon nan na yin gaban kai yana mai ba da fifiko ga musayar yawu. Kazalika ya sassauta takunkumi kan ƙasar Cuba ya gabatar da matakan janye sojojin Amirka daga Iraƙi sannan ya dakatar da shawarar dirke makaman garkuwa ga makamai masu linzami a samaniyar ƙasashen gabacin Turai. Kuma kasancewar ana samun banbancin martanin da ake mayarwa game da waɗannan manufofi, ba shakka abu ne dake yin nuni da cewar hatta shugaban Amirka, shi kaɗai, ba zai iya warware matsalolin da ake fama da su a wannan duniya da tuni ta zama rufa ɗaya ba.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu