1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon Jamus ga kasar Haiti

January 14, 2010

Jamus ta aika da kayan agaji da ma'aikatan ceto zuwa Haiti bayan girgizar kasa a can

https://p.dw.com/p/LVbT
Barnar girgizar kasa a HaitiHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Jamus ta aika da agaji na Yuro miliyan ɗaya, don bada agajin gaggawa ga waɗanda girgizar ƙasar ya shafa a ƙasar Haiti. A wata wasiƙar da ministan harkokin wajen Jamus Westerwelle ya aika, ya kwatanta abun da wani bala'ine wanda ya zama wajibi gwamnatin Jamus ta kai ɗauki. Usman Shehu Usman na da ci gaban rohoto.

An amince da batun agajinne bayan da majalisar zartarwar gwamnatin Jamus ta yi wani zama a Berlin, Inda nan take suka amince da batun kai ɗauki ga ƙasar Haiti wanda bala'in girgizar ƙasa ya aukawa. Kakakin gwamnatin Jamus Wilhem ya yi ƙari harke bisa taimakon da Jamus ta aika da shi.

Shugabar gwamnatin Jamus ta samu labarin wannan girgizar ƙasar wanda kuma ya kaɗa mata zuciya. Muna taya waɗanda abin ya shafa da ma yan uwansu jimamin abin da ya faru, kana muna basu goyon baya. Shugabar gwamnatin Jamus ta jaljantawa shugaban ƙasar Haiti, kana ta aika da taimako ga ƙasar ta Haiti, wanda gwamnati Jamus tayi"

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya tattauna da jakadan ƙasar Jamus dake a birnin Port-au-Prince, inda ya bayyana masa kaɗuwar da ya yi bisa wannan bala'in.

Muna yin jimami tareda al'ummar ƙasar Haiti, dama waɗanda girgizar ƙasar ta shafa, Gwamnatin Jamsu za ta bada duk abinda za ta iya bayarwa, kana muna baiwa yan ƙasar Haiti goyon baya, zamu kuma taimaka musu"

Taimakon Yuro miliyan ɗaya da aka bayar cikin gaggawa zai taimaka gaya, a aikin sheto da akeyi bisa wannan mummunan girgizar ƙasa, wannan kuɗin dai an bayar da sune ta hannun ƙungiyoyin agaji na ƙasar ta Jamus waɗanda ke da ma'aikatansu yanzu haka a ƙasar ta Haiti don bada agaji, Kana kuma Jamus za ta bada agajin sake gina ƙasar, amma yanzu abinda aka fi buƙata cikin gaggawa shine kuɗi. Yanzu haka dai ƙugiyoyin agajin sun aika da kwararrun mutane kamar yadda kakin ma'aikatar cikin gida Stefan Paris yace.

"Kungiyoyin sune SEBA da SEWA waɗanda ke da ƙwarewa wajen aikin ceto ga misali SEWA ƙungiyace dake taimako wajen sake gina ƙasa, da samar da ruwa, ma'ana dai yanzu a aikin sheton da akeyi, ƙungiyar za ta yi aiki wajen samar da ruwan sha. Daga bisani sai su ci gaba da wani taimako na daban"

Ita ma ma'aikata bada taimako da raya ƙasashe ta nan Jamus tana aiki tuƙuru, domin yanzu haka ta aika da kayan abincin wanda ya kai na yuro dubu 500.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu