1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya

January 7, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta samo sunanta ne daga Shugaban Amirka Franklin Roosevelt a ranar 1 ga watan janairun shekara ta 1942 a lokacin yaƙin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/LNpl
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon a taron manema labaraiHoto: AP

Bayan da ƙasashe 26 suka amince su ci gaba da yaƙi da dakarun Hitler da ƙawayen sa. Kafin dai kafuwan Majalisar Ɗinkin Duniyan akwai ƙungiyar League of Nations da aka kafa bayan kammala yaƙin Duniya na farko. To sai dai ƙungiyar ta ruguje bayan da ta kasa hana aukuwan yaƙin duniya na biyu.

Koda yake kafin kafuwan Majalisar ta Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi da aka kafa domin haɗin kai da cigaban ƙasashen na duniya, irin su ƙungiyar ma'aikatan sadarwa ta ƙasa da ƙasa a 1865 da kuma ƙungiyar ma'aikatan gidajen wasiƙu a 1874. Wa'yanda daga bisani suka rikiɗe zuwa hukumomin Majalisar ta Ɗinkin Duniya bayan da aka kafa ta.

Taron farko da aka gudanar a ƙarƙashin lemar Majalisar Ɗinkin Duniya itace wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shine yakai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a ƙasar Holland a 1902.

A 1945 ne ƙasashen duniya 50 suka gudanar da taro a Jihar San Francisco na Amirka domin ƙaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun haɗa da Amirka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa, wa'yannan ƙasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu ƙarfin faɗa aji.

A ranar 24 ga watan Oktoban 1945 ne dai wa'yannan ƙasashe suka rattaba hannu a daftarin ƙarshe da ya kafa Majalisar ta Ɗinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar 24 ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta. Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru 64 da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwan ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma maici yanzu Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu.

Mawallafi: Babangiga Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal