1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya karɓi lambar yabo ta Nobel

Abdullahi Tanko BalaDecember 10, 2009

Obama ya karɓi lambar yabo ta Nobel bisa yunƙurinsa na wanzar da zaman lafiya a duniya

https://p.dw.com/p/KzMP
Shugaba Barack ObamaHoto: AP

A yau a birnin Oslo aka baiwa shugaban Amurka Barack Obama lambar yabo ta Nobel bisa yunƙurin da ya nuna na samar da wanzuwar zaman lafiya da lumana a duniya.

Obama / Nobelpreis / Oslo
Shugaba Barack Obama tare da shugaban kwamitin bada kyautar yabon ta Nobel Thorbjorn Jagland yayin bikin bada lambar yabon a OsloHoto: AP

Jawabin da ya gabatar a birnin Alkahira inda ya buƙaci samar da sabuwar dangantaka da ƙasashen Musulmi da kuma burin sa na kawar da muggan makaman Nukiliya daga doron ƙasa sun jawo masa martaba da daraja a idanun alúmar duniya sai dai kuma manazarta na ganin akwai jan aiki wajen cimma wannan nasara.

Baa dai taba samun shugaban da ya karɓi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ba a ɗan taƙaitaccen lokaci da yake shirin tura dakarun soji 30,000 zuwa fagen daga ba sai a wannan karon. " Obama yace buƙata ce muhimmiya a gare mu da ƙasa baki ɗaya, mu tura ƙarin dakarun soji 30,000 zuwa Afghanistan".

Wannan yaƙi ne dake da muradin kare su kansu ƙasashen musulmi, domin kuwa sojojin suna yaƙi ne da yan Al-Qaída da kuma yan Taliban masu matsanancin raáyi a Afghanistan a cewar wani jamií na Obama. Ya ƙara da cewa shugaban yana da kyawawan manufofi da hangen nesa waɗanda dukkanin su ke da nufin samar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Wani mai raáyin riƙau kuma ɗan Jamíyar Republican kana tsohon muƙaddashin sakataren tsaro a zamanin gwamnatin George W Bush Paul Wolfowitz shima ya yaba da matsayin hangen nesa na shugaba Obama." Barack Obama na da damammaki masu yawa saboda yana da kyakyawar zuciya da manufa mai kyau saboda matsayin sa da kuma burin da yake da shi ga Amurka".

Capitol Hill in Washington
Fadar gwamnatin AmurkaHoto: Illuscope

Manufofin Obama na harkokin waje sun dogara ne ga irin namijin ƙoƙarin da zai nuna da kuma ya jajircewa wajen sauya manufofin magabacinsa George W Bush a cewar tsohon wani tsohon jakadan Amurka Nicolas Burns." A yanzu abin da shugaba Obama yake son yayi shine ƙirƙiro da sabuwar hanyar Diplomasiyya".

Wata manufar ta Obama ita ce tattaunawa ba tare da gindaya sharuɗa ba, walau da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Il ko kuma shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad, idan ma da hali da yan Taliban masu sassaucin raáyi. Sai dai a waje guda shugaban na Amurka bai ɓoye fushinsa na cewa haƙurin sa na da iyaka ba, musamman idan aka zo ga batun Nukiliyar Iran. Wannan kuwa sun haɗa da sanya mata tsauraran takunkumi da maida ita saniyar ware da ma kuma yiwuwar ɗaukar matakan soji akanta.

Sai dai waɗannan kurari ko barazana a cewar wani masanin kimiyyar siyasa Daniel Senor har yanzu ƙasar Iran taki cewa kome. Yayin da a waje guda Iran ke amfani da salon jinkirta tattaunawar, a ɗaya ɓangaren Obama na ƙoƙarin kaucema sake shigar da Amurka cikin wani yakin na uku.

US-Truppen in Südkorea
Sojin Amurka a filin DagaHoto: AP

Bayan yake yaken Iraqi dana Afghanistan, yayin da a gefe guda ya kwana da sanin cewa Israila ba zata sakar masa mara ba inda take dukkan bakin ƙoƙari na kassara yunƙurinsa na shirin wanzar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya. Ko da yake a cewar Obaman an sami cigaba mai maána a wannan ɓangaren.

Sai dai Obama yana sane da cewa shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ɗaya daga cikin muhimman mutanen da yake tattaunawa da su a Gabas Ta Tsakiya ya yanke ƙauna game da samun wani sauyi, yayin da a ɗaya ɓangaren Firaministan Israila Benjamin Netanyahu bai da niyyar dakatar da faɗaɗa matsugunan Yahudawa, kana bashi da shaáwar aiwatar da masalahar nan ta kafa ƙasashe biyu da zasu zauna daura da juna cikin lumana da girmamawa.

A jawabin da yayi a lokacin da ya kai ziyara Masar watanni uku bayan da ya hau karagar mulki Obama yayi bayani yana mai cewa " Na zo nan Alƙahira ne domin samar da wanzuwar sabuwar dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen musulmi a faɗin duniya.

Jawabin ƙarfafa dangantaka da ƙasashen musulmi da kuma buƙatar da ya gabatar a birnin Prague na kawar da makaman Nukiliya daga doron ƙasa, a ƙarshen shekarar farko na mulkinsa wajibi ne Obama ya nuna cewa ƙudirinsa na sauya fasalin alámuran duniya basu kasance bayanai na fatar baka ba.

Mawallafa : Sina, Ralp / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Ahmed Tijani Lawal