1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Siyasa | 04.11.2009

Jawabin Merkel ga majalisar wakilan Amirka

 

Angela Merkel ta kasance wata shugabar gwamnatin Jamus ta farko da ta yi jawabi gaban majalisar dokokin Amirka bayan Konrad Adenauer a shekara ta 1957

 

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ta fara ganawa da shugaba Barak Obama na Amirka gabannin yiwa zaman haɗin gwiwar majalisun dokokin ƙasar jawabi - a dai dai lokacin da ƙasarta ke shirye shiryen gudanar da shagulgular cika shekaru ashirin da faɗuwar katangar Berlin - katangar da a baya ta rabe tsakanin gabashi da kuma yammacin Jamus, ta miƙa godiyarta ga Amirka bisa rawar data taka wajen haɗewar yankunan biyu:Merkel a majalisar dokokin AmirkaBildunterschrift: Merkel a majalisar dokokin Amirka

" Ina so ku bani dama in nuna cewar mu Jamusawa muna sane da irin abubuwan da ku, abokan mu Amerikawa kuka yi mana. Har abada  ni kaina musamman ba zan taɓa mantawa  da hakan ba."

Jawabin na Merkel, ya kuma taɓo batun dunƙulewar duniya wuri guda, game da buƙatar yin saiki tare:

" Har a wnanan lokaci, cikin ƙarni na  21,  kuma a zamanin  da duniya ta zama gida ɗaya; al'umma ɗaya, babu abin da ba za'a iya aiwatar dashi ba. A can gida a Jamus da kuma a nan gaba ɗaya mun san cewar   batun maida duniya ƙauye ɗaya, abune dake kawo damuwa da tsoro a zuƙatan jama'a. Wannan kuwa hali ne da ba zamu  yi watsi dashi ba. Muna sane da wahalolin dake akwai, to amma  alhakin mu ne mu ja hankalin  jama'a, mu nuna masu cewar ƙoƙarin maida  duiya ta zama ƙauye ɗaya,  wata babbar dama ce ga ko wace nahiya. Saboda hakan zai tilastawa duka kasashe su  haɗa gwiwa su riƙa  yin komai tare. Rashin samun wannan haɗin kai babu abin da zai haddasa, illa koma baya, ƙaruwar talauci  da kuma maida kasashe su zama saniyar-ware. Muna sane da cewar  Turai da Amerika ba ko wane lokacine suke da ra'ayoyi iri ɗaya ba. Wani lokaci  mu kan zargi junan mu da laifin tsoro ko  jan kafa a wasu al'amura, to amma  nayi imanin cewar babu wata ƙawa da ta dace da  Turai  fiye da Amerika, babu wata ƙawa da ta dace da Amerika irin Turai."

Data juya ga fafutukar yaƙi da masu tada tarzoma kuwa, Merkel ta ce, Jamus ta ƙuduri anniyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Amirka a wannan fannin ma:

" Muna iyakacin ƙoƙarin mu a  matakan yaƙi da aiyukan tarzoma a duniya baki ɗaya. Muna kuma sane da cewar babu wata ƙasa, komai ƙarfin ta da zata sami nasarar wannan yaƙi ita kaɗai. Dukkan mu gaba ɗaya muna buƙatar abokan haɗin gwiwa, inda sai tare da wannan haɗin kai ne  zamu nuna  ƙarfin mu. Saboda haka ne a bayan hare-haren ranar  11 ga watan Satumba, muka daidaita tare da tsohon shugaban Amerika, George Bush cewar  nan gaba, ba zamu sake yarda Afghanistan ta  ta zama cibiyar da zata  haddasa haɗari ga tsaro da zaman lafiyar duniya ba. Jamus saboda haka   ta kasance  ƙasa ta ukku da suka fi yawan  sojoji a ƙasar ta Afghanistan.  Burin mu shine ganin  matakan  soja da na farar  hula sun kai ga samun nasarar   hana  aiyukan tarzoma daga  ƙasar ta Afghanistan. Babu shakka aiyukan da  rundunar ƙasashen duniya take yi a Afghanistan  suna da tsanani, to amma da zaran  sabuwar gwamnatin da aka zaɓa a ƙasar ta  kama mulki, wajibi ne a  aiwatar da  sabuwar manufar da zamu tsara. Manufar wannan shiri  ita ce ɓullo da wani tsari inda 'yan Afghanistan sannu a hankali zasu sami ƙarfi  aiyukan tafiyar da  mulki da tsaron ƙasar su da kansu. Wannan tsari kuwa zamu shimfiɗa shi ne a lokacin wani  wani taro na Majalisar Ɗinkin Duniya a farkon shekara mai zuwa. Ba kuwa zamu sami nasarar aiwatar da  shirin ba, sai idan  mun haɗa gwiwa a ko wane mataki zamu dauka. Jamus ba zata  kaucewa ɗaukar wannan nauyi ba."Majalisar dokokin Amirka a Washington D.C.Bildunterschrift: Majalisar dokokin Amirka a Washington D.C.

Merkel, ta kuma yaba da rawar da Amirka ke takawa wajen shawo kan matsalar ɗumamar yanayi a duniya:

" Ina farin cikin ganin cewar  shugaba Obama  da ku kanku a aiyukan ku, kuna bada muhimmanci ga matakan kare  kewayen ɗan Adam. Gaba ɗaya muna sane da cewar  bamu da sauran lokacin da zamu ɓata. Muna buƙatar daidaituwa kan batun  kare muhalli a lokacin  taron da za'a yi a Copenhagen a watan Disamba. Burin mu shine ganin  an rage  ɗumamar yanayin sararin samaniya.  Samun nasarar haka  yana buƙatar  haɗin kan mu gaba ɗaya da cika alƙawura idan aka yi su. Kaucewa duk wani ƙoƙari na cika wannan buri ba abu ne da zai  dace ba a  ƙoƙarin kare muhallin mu. Muna buƙatar ɓullo da sabbin fasahohi, waɗanda  zasu iya zama wata babbar dama ta samun bunƙasar  tattalin arziƙin mu da kare wuraren aikin yi."

A wannan larabar ce dai, Merkel ke kammala wannan ziyarar ta yini biyu a ƙasar ta Amirka.

Mwallafi: Umar Saleh

Ediwa: Umaru Aliyu

 
 

Send us an e-mail »Send »Print »

More on the topic

 
Share this article


 
Picture of the Day
ImageOfTheDay

DW-TV EUROPE live

drive it! - The Motor Magazine

We're sorry, due to legal issues this content can not be transmitted as live stream.

If you are inside the United States, it is still possible for you to enjoy DW-TV. For more information, please click here.