1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Obama a Rasha

July 7, 2009

Obama da Medvedev sun rattaba hannu a ɓangaren farko na yarjejeniyar rage makaman nukiliya.

https://p.dw.com/p/IifR
Medvedev da ObamaHoto: AP

A wannan ziyar dai ƙasar Rasha ta yi wa shugaban Amirkan Barack Obama bazata inda ta miƙa masa wasu takardun da Tsar Alexander II da takwaransa na Amirka a waccan lokacin Abraham Lincoln suka rattaba hannu a kai.

Daga cikin jadawalin ganawar tasu a yau dai shi ne ƙayyade yaɗuwar makaman nukiliya da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, wanda ta yi tsami zamanin mulkin tsohon shugaba George W. Bush na Amirka. Shugaba Barack Obama ya ce yanzu abin da ya kamata shi ne amanta da baya a gina gaba.

Obama ya ce "Yanayin tinkarar juna irin na zamanin yaƙin cacar baka ya zama tsohon yayi. Yanzu lokaci ne da ya kamata a buɗe wani sabon babi, Ina ganin Medvedev ya fahimci hakan. Ina ganin Priminista Putin yana da hannu a tsohon hulɗarmu, kuma a yanzu ma yana da rawar da zai taka a wannan sabuwar ma".

Shugabannin na Rasha da Amirka sun amince da farfarɗo da wata hukuma wadda za ta riƙa kula da hulɗa tsakaninsu. Hukumar wadda tun a shekara ta 1992 aka kafa ta, to amma dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu, a wani yunƙurin da Amirka ta yi, na kafa na'urar kariya daga makamai masu linzami, a wasu ƙasashen gabashin Turai masu maƙobtaka da Rasha, abin da Rasha ke ganin wata barazana ce a gareta.

Shugaban ƙasar Rasha Dmitri Medvedev, shi ma ya nuna muhimmancin dangantakar ƙasashen biyu. Medvedev ya ce "yana da muhimmancin gaske a samu sassautawa don kafa hulɗa mai inganci tsakaninmu. Ta haka sai a samu amincewa da yarjejeniya wajen rage yaɗuwar makaman nukiliya. Daga bisani sai a samu bai ɗaya fahimtar juna, kamar yadda zamu tinkari batun shirin Amirka na kafa na'urar kariya daga makamai da take son kafawa".

Manyan ayyukan hukumar da shugabannin suka farfaɗo da ita, su ne ta warware batun rikinci yaƙin duniya na biyu da yaƙin Koriya, dama na Vietnam sai kuma yaƙin tarrayar Soviet a Afganistan. Waɗannan sune abin da za a waraware zare da abawa a game dasu. Ta yadda waɗannan ƙasashen za su kafa wata dawammamiyar hulɗa.

Ƙasar Rasha da Amirka dai sun daɗe suna cancar baki a tarihance tsakanin su, duk dacewa hakanan bata taɓa kai su ga gwabza yaƙi ba. To amma kowacce ta mallaki makaman kare kai daga juna.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abba Bashir