1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

040609 Obama Rede Reax

June 5, 2009

Har yanzu ƙasashen duniya na ci-gaba da furta albarkacin bakinsu game da jawabin da shugaban Amirka Barack Obama ya yi jiya a birnin Alƙahira inda ya yi kira da a buɗe sabon babin dangantaka da ƙasashen Musulmi.

https://p.dw.com/p/I44C
Barack ObamaHoto: AP

Isra´ila ma da Falasɗinawa su ma sun mayar da martani to sai dai ra´ayoyinsu sun bambamta da juna.

A cikin wata sanarwa da ta bayar a birnin Ƙudus gwamnatin Isra´ila ta ce kamar shugaba Barack Obama ita ma tana da kyakkyawan fatan samun zaman lafiya da ƙasashen Larabawa. Ta bayyana jawabin na Obama da cewa muhimmi ne wanda ta yi fata zai kai ga buɗe sabon babin yin sulhu tsakanin Isra´ila da ƙasashen Larabawa da na Musulmi.

To sai dai ra´ayoyin ´ya´yan gwamnatin ƙawance ƙarƙashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu sun bambamta. Yayin da Minista Avishai Braverman na jam´iyar Labour ya yaba da jawabin shugaban na Amirka musamman dangane da yin sulhu na ƙasashe biyu, shi kuwa ministan kimiyya Daniel Hershkowitz na jam´iyar masu matsanancin ra´ayin kishin Yahudawa bai nuna gamsuwa ba yana mai cewa dangantaka da Amirka ta ta´allaka ne kan abokantaka amma ba matsa mata lamba ba. Masani kan manufofin ƙetare na jam´iyar Likud dake jan ragamar mulki Zalman Shoval ya yi takatsantsan a martanin da ya mayar.

"Babu wata gwamnatin Isra´ila da ke yanke shawara saboda jawabin wani ɗan siyasar Amirka illa saboda abinda ke zama muhimmi a gareta. Hasali ma ai Obama bai faɗi sabon abu ba a jawabin nasa."

Ita kuwa jam´iyar adawa ta Kadima na ganin an sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi musamman game da ƙin da Netanyahu yayi na yin sulhun kafa ƙasashe biyu.

A daura da haka shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas yabawa yayi inda kakakinsa Saab Erekat ya ce jawabin na Obama muhimmin mataki ne akan turbar da ta dace.

"Jawabin Obama ya share hanyar samar da ƙasashe biyu maƙwabtan juna. Fata na shi ne shugaba Obama ya gabatar da takamammen tsari da lokaci tare da masu sa ido na ganin wannan shiri na kafa ƙasashen biyu ya tabbata."

Sauran talakawan Falasɗinu da suka saurari jawabin su ma sun nuna gamsuwarsu kamar yadda wannan mutumin a Gaɓar Yamma da kogin Jordan ya nunar.

"Obama na iya matsa ƙaimi akan Isra´ila domin samar da kyakkyawan yanayin tattauna batun zaman lafiya wanda zai kai ga samun sakamako na gari a wannan yankin."

Su ma Falasɗinawa a Zirin Gaza musamman matasa sun yaba da jawabin kamar yadda wannan matashi ɗan shekaru 23 ya nunar:

"Na ji daɗi jawabin domin ya yaba da addinin musulunci kuma bisa ga dukkan alamu Obama na son ya buɗe sabon babi musulmi. Saɓanin magabacinsa Goerge W Bush, Obama ya yi magana ƙarara game da dakatar da gina matsugunan Yahudawa da daina tashe tashen hankulan Falasɗinawa."

Kamar yadda da ma aka yi zato ƙungiyar Hamas dake mulki a Gaza ta nuna shakku ga jawabin duk da fatan da ta yi, amma kakakinta ya ce kamata yayi shugaban na Amirka ya girmama nasarar zaɓen da Hamas ɗin ta samu a Gaza.

Mawallafa: Clemens Verenkotte/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed