1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barack Obama gaban ´yan jarida

March 25, 2009

Shugaban Amurika ya tattana da ´yan jarida

https://p.dw.com/p/HJLh
Obama yayi taron manema labaraiHoto: AP

A wannan taron manema labarai shugaba Barack Obama ya taɓo batutuwa dabam dabam da suka shafi tattalin arziki, rikicin nukleyar ƙasar Iran.

Barack Obama yace gwamnatinsa ta gaji matsaloli a fannoni dabam-dabam na rayuwar Amurikawa ko wane fanni, to saidai akwai haske a yunƙurin da ake a halin yanzu na magance su.

Sannan ya kare tsarin kasafin kuɗin da yayi, na dalla Triliyan 3,6, wanda a cewarsa shine tubalin da Amurika zata yi dogaro kansa, domin fita daga gacci.


"Fassalin kuɗin da na gabatarawa Majalisa, nayi imanin zai farfaɗo da tattalin arzikin Amurika, ta yadda za mu iya kaucewa matsala mummunan irin wadda muka shiga yanzu.

Babu shakka zamu fita daga wannan ƙangi amma abin zai ɗauki lokaci, kuma yana buƙatar haƙuri da haɗin kai da jajircewa".

Shugaba Barack Obama yai ce babu sasauci ga miyagun shugabanin kamfanoni da masana´antu da kuma masu hada hadar hannayen jari dake buƙatar arzuta kansu ta kowane hali.

Wannan kalami da Obama, na matsayin tuni ga matakin da ya ɗauka na haramta ƙarin albashi da shugabanin kamfanin inshora na AIG suka yiwa kansu, a daidai lokacin da gwamnati ta saka tsabar kuɗi fiye da dalla miliyan 160 domin ceton kamfanin da ya shiga halin mutu kwakwai rai kwakwai.

Jawabin na shugaban Amurika, ya zo kwanaki kaɗan, kamin taron shugabanin ƙasashen G20, wato ƙasashe 20 da suka fi samun cigaba a duniya, da zai gudana wata mai kamawa a birnin London na Bitaniya, saboda ya bukaci ayi amfani da wannan taro domin magance matsalar durƙushewar tattalin arziki da ta zama ruwan dare gama duniya:Shawarata itace ya kamata ko wace kasa ta bada haɗin kai domin fita daga wannan ƙangi, wato ko wace ƙasa tayi iya ƙoƙarinta, kar ta gama hannu tayi jiran wata ƙasa tazo ta fidda ta daga cikin wannan matsala.

A ɗaya wajen, ya bayyana wajibcin ƙara bada kula ta mussamman ga ɓangarorin kiwan lafiya, ilimi ,da makamashi.

A game da harakokin diplomatiya, Obama ya bayyana fatan Iran zata karɓi tayin da yayi mata, na warware taƙƙadamar nuklear cikin ruwan sanhi.

Kazalika ya dangata hawan Benjamin Nitenyahu a kujera Firamisnitan Isra´ila, a matsayin wani mataki na kaiwa ga zaman lafiya mai ɗorewa a yankin gabas ta tsakiya. Ya kuma jaddada burin Amurika na samar da ƙasashe guda biyu, wato Isra´ila da Palestinu, wanda za su maƙwabtaka cikin girmada arziki ta hanyar cuɗe ni in cuɗe ka.

Mawallafa: Yahouza Sadissou Madobi/ Christina

Edita : Umaru Aliyu



,