1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Amina sarauniyar Zazzau

Abba BashirMarch 23, 2009

Taƙaitaccen tarihin rayuwar Amina sarauniyar Zazzau

https://p.dw.com/p/HHth
Tutar Najeriya

Tambaya: Fatawar farko a shirin namu ta fito daga hannun malama Maimuna Yakubu Nuhu daga Jihar Gombe a tarayyar Najeriya. Malamar cewa ta yi; Ku ba ni tarihin rayuwar Amina sarauniyar Zazzau wato “Queen Amina”, a ina ta rasu, kuma a ina kabarinta yake a halin yanzu. Shin akwai sauran zuriyarta kuwa a ƙasar Zazzau.

Amsa: To dangane da wannan tambaya, mun tuntuɓi Ahmad Adamu, masanin tarihi a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a Najeriya.

Adamu: Amina Sarauniyar Zazzau, wadda ta rayu daga shekarar 1533 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa 1522, wato shekarunta 13 ke nan akan karagar mulki. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.

Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta yi kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Idan aka ɗauki tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja akwai ƙananan garuwa da dama da sarauniya Amina ta kafa, sai dai ba masu girma ba ne, saboda kamar dai wurare ne da ta ci zango a wajen.

Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarinta ya ke ba.

Idan aka koma ga maganar zuriyar sarauniya Amina, a gaskiya abu ne mai wuya ace ga waɗansu da suke zuriyarta ne, tun da agaskiya yadda tarihi ya nuna, sarauniya Amina har ta mutu ba ta yi aure ba. Don haka babu wata shaida dake nuna cewa a ciki ko wajen zazzau, akwai wasu da za a iya cewa zuriyarta ne.

To sai dai duk da cewa, akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce, Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa, a matsayin sarauniya a Zazzau.