1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

180209 Dialog Immigrantenstadl Köln

Mohammad AwalFebruary 25, 2009

A ranar Litinin da ta gabata aka kawo ƙarshen bukin al´adu na Karnival na bana a yankunan dake bakin kogin Rhein na nan Jamus.

https://p.dw.com/p/H1FK
Jerin gwanon masu bukin Karnival a KolonHoto: AP

A ranar Litinin da ta gabata aka kawo ƙarshen bukin al´adu na Karnival na bana a yankunan dake bakin kogin Rhein na nan Jamus. Bukin dai ya fi yin armashi ne a birnin Kolon dake zaman cibiyar bukin Karnival a Jamus baki ɗaya. Su ma baƙi dake a wannan birni ba a barsu a baya ba wajen shiga a dama da su a bukin a matsayin wani ɓangaren na rungumar al´adun Jamusawa. Shirin na yau dai zai duba irin rawar da baƙin ke takawa ne a wannan buki mai muhimmanci ga dukkan nen birane da garuruwan dake a bakin kogin na Rhein.

Deutschland Karneval Rosenmontag Köln
Hoto: AP

Rungumar al´adun wasu al´umomin dai na da fuskoki da dama. Shiga cikin bukin Karneval ma na daga cikin waɗannan fuskokin musamman ga waɗanda ba ´yan asalin yankin da ake wannan buki ba wato kamar a birnin Kolon. A wannan birni dake zama mafi girma a jerin biranen Jamus dake gudanar da wannan buki, wasu baƙi daga ƙasashen ƙetare da kuma wasu yankuna na Jamus, amma haifaffun wannan birni suna da ta su ƙungiyar ta Karnival wadda suka kafa ta kimanin shekaru huɗu da suka wuce.

Imi shi ne laƙabin da ake yiwa duk wanda ba haifaffen birnin Kolon ba ne wato ko Baturke ne shi ko Ba-Amirke ne shi ko kuma daga wata jiha ta Jamus ya fito. Wannan kalmar dai ba wai ana amfani da ita ne don ƙasƙantar da wani ba. Akwai dai ire-iren waɗannan baƙi da yawa a birnin na Kolon, inda alƙalumman suka nuna cewa kashi ɗaya cikin uku na mazauna wannan birni suna da asali da ƙasashen waje.

Deutschland Karneval Rosenmontag Köln Paris Hilton und Amy Winehouse
Hoto: AP

Bukin Karnival dai wani muhimmin ɓangare ne a fannin a al´adu da zamantakewa tsakanin mazauna wannan birni. Ga baƙi ´yan ƙaƙagida waɗanda tun shekaru da yawa da suka wuce suka mayar da birnin matsayin wata ƙasarsu ta biyu suna tinƙaho da bukin na Karnival a Kolon. Kimanin shekaru huɗu da suka wuce wasu baƙi ´yan fasaha a birnin suka gudanar da na su bukin. Todor Bogdanovic mawaƙi ne kuma ɗan wasan kwaikwayo ɗan asalin ƙasar Montenegro amma yake amfani da takardar fasfo na Sloveniya ya ce an wancan lokaci an gabatar da shawarwari da dama don kafa ƙungiyar Karnival ga baƙi.

“A lokacin da muka fara zaman shawarwarin kafa wannan ƙungiya wani ya yi tambaya ko da akwai wani daga cikinmu da ya fito daga Kolon? Ba wanda ya ba shi amsa. Wani ya furta cewa wannan zama ne na baƙi tsantsa, daga nan aka samu sunan ƙungiyar Karnival ga baƙi.”

Wannan ƙungiyar ta yi ta shirya tarukan Karnival a Kolon ba tare da ´yan asalin wannan birni ba. Ta ƙunshi ´yan wasannin kwaikwayo da makiɗan gargajiya daga ƙasashe kamar Turkiya da Girika sai kuma ´yan dirama daga wasu yankuna na Jamus da kuma ƙasashen waje. Ba sabon abu ne idan a cikin wannan ƙungiyar wata a cikin lulluɓi ta yi kwaikwayon iri masu wasannin Karnival ko fitattun ´yan siyasa ko dai wani batu dake ɗaukar hankalin jama´a ko kuma yin barkwanci don nishaɗantarwa.

´Yan bukin Karnival dake a cikin wannan ƙungiyar dake da asali da baƙin ´yan ƙasashen waje, suna wasanni iri-iri musamman game da batutuwan da suka shafi zaman baƙi a nan ƙasar, waɗanda ba safai ne ake fitowa fili a faɗe su ba. Suna nuna jin daɗinsu ga wannan matakin da suka ɗauka domin sajewa da ´yan ƙasa musamman a wannan lokacin da ake zargin cewa baƙi mazauna a wannan ƙasa suna fatali da salon rayuwa da kuma al´adun Jamusawa.

Büllent Yilmaz Bajamushe mai asali da ƙasar Turkiya, wanda tun a cikin shekarun 1960 iyayensa suka yi ƙaura zuwa Jamus a matsayin ´yan ci-rani ya yi bayani yana mai cewa.

“Mu kan yiwa juna barkwanci don kawai mu yiwa junanmu dariya. Mu kan yi haka ne don faɗakar da sauran jama´a game da batun ƙaƙagida da kuma sajewa da mutane gari domin su ɗauki wannan batu da muhimmanci. Muna wayar da jama´a kai game da batutuwa da dama kamar kyautata zamantakewa da daraja al´adun juna.”

Wata ƙungiya dake kiran kanta Annashuwa cikin Zamantakewa ita ke ɗaukan nauyin wasannin da ƙungiyar Karnival ta baƙi ke yi. Shugaban ƙungiyar Hektor Haarkötter ya ce burinsu shi ne samun wani kyakkyawan tsarin zamantakewa.

“A cikin wannan ƙungiyar akwai mutane waɗanda saboda bambamcin asalinsu da addininsu da al´adunsu da wataƙila ba su haɗa kai don gudanar da wannan gagarumin aiki ba. A cikin wannan ƙungiyar za ka tarar Baturkiya tana rawa tare da ´yar Girika, ko musulmi yana aiki tare da Kirista ko Bature yana mu´alala ta kurkusa da wanda ba Bature ba. Wannan shi ne abin da muke nunawa duniya wato ba ruwanmu da banbancin jinsi ko addini, a garemu kowa ɗaya ne kuma samun irin wannan haɗin kai abin sha´awa ne.”

Ga mutane da yawa lokacin bukin Karnival wata dama ce a garesu na yin wani ado daban ko sauya kamaninsa na wani gajeren lokaci. Katja Solange Wiesner ´yar wasan kwaikwayo ce wadda ke da ruwa biyu, wato Jamus da kuma Kamaru. Kasancewarta wankan tarwaɗa tana amfani da wannan damar don rikitar da jama´a game da asalinta a lokacin na bukin Karnival.

Deutschland Karneval Rosenmontag Mainz Clown auf Fahrrad
Hoto: AP

“Kamanni na bai yi kama da Bajamushiya ko ´yar Kolon ba, ko da yake ni ´yar nan garin ce. Shi ya sa ina ganin muhimmin abu ne in nunar da haka. Ina jin daɗi ƙwarai da gaske idan na ɓadda kama na yi lulluɓi don nunawa jama´a cewa akwai musulmi da yawa waɗanda aka haife su a nan, suke magana da karin harshen ´yan Kolon kuma suka saje da ´yan ƙasa. To amma ana nuna musu wariya saboda fuskokinsu sun banbanta. Ni ma ina fuskantar irin wannan matsala saboda launin fatar jiki na duk da cewa ni Bajamushiya ce.”

A ranar Litinin da ta gabata bukin na Karvival a wannan shekara ya kai ƙololuwarsa inda a cikin ado masu launuka iri daban-daban mutane suka gudanar da fareti da waƙoƙi da kaɗe-kaɗe na badujala daban daban a dukkan birane da garuruwa dake a yankin tekun Rhein.