Zamantakewa | 13.02.2009
Bukin nuna al´adun gargajiya na al´umar Kalabari
A kwanakin baya al´umar gundumar Kalabari dake a yankin Niger Delta mai arzikin ma fetir dake a tarayyar Nijeriya suka gudanar da wani kasaitaccen bukin nuna al´adunsu na gargajiya da suka gada kaka da kakanni. Basaraken wannan masarauta ta Kalabari Farfesa Princewill ya gayyaci baƙi daga ciki da wajen yankin don su taya al´umarsa murnar gudanar da wannan buki.


















