1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta yaya Hawainiya ke haihuwa

Abba BashirDecember 1, 2008

Takaitaccen bayani a game da yadda hawainiya take haihuwa

https://p.dw.com/p/G7Do
Hawainiya mata da mijiHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Hafsatu Abubakar Hamza daga Jidda a Ƙasar Saudiyya. Malamar cewa ta yi, wai shin ta yaya hawainiya take haihuwa, ƙwai take yi kamar na ƙadangare ko kuwa haihuwa take yi? Da fatan zaku ba ni gamsasshiyar amsa.



Amsa: Hawainiya ɗaya ce daga cikin halittun da Allah ya halitta a doron ƙasa. Kuma babu shakka akwai abin al'ajabi game da yadda hawainiya take haihuwar 'ya'yanta, da kuma hanyar da 'ya'yan nata suke zuwa duniya. Kuma ko shakka babu akwai darasi da ɗan Adam ya kamata ya ɗauka daga tsarin haihuwar hawainiya.


Da farko dai, idan hawainiya ta ɗauki ciki, to namijin ne zai je ya haƙa rami, ita kuma ta matar sai ta zo namijin ya binne ta a ramin da ranta. Wani lokaci takan shiga salin alin, wani lokaci kuma sai sun yi kokawa da namijin ya galaɓaitar da ita, sannan ya tura ta cikin ramin ya binne ta. A haka za ta mutu ta ruɓe, 'ya'yan cikin nata su ƙyanƙyashe sannan su fito duniya. Kuma ko da ruwan gatari ko wani ƙarfe mai faɗi aka sa a kan kabarin nata, idan dai lokacin fitowar 'ya'yan ya yi, haka za su huda wannan ruwan gatarin ko ƙarfen su fito. Kuma tun da Allah ya halicci hawainiya haka take haihuwa bata taɓa fasawa ba.


Darasin da ke tattare da tsarin haihuwar hawainiya shi ne cewa, babu wata hawainiya da ta taɓa morar ɗanta a duniya, tun da sai ta mutu sanan 'ya'yanta suke zuwa duniya. To ina ga ɗan Adam,  kai da Allah ya ƙaddara zaka haifi 'ya'yanka, su girma, har ka riƙa alfahari da su, amma sai mutum ya riƙa watsi da 'ya'yansa, bai ma damu da rayuwarsu ba. Yau da ace ta hanyar da hawainiya take haihuwa, haka ma ɗan Adam yake haihuwa, ina mutum zai kai ƙara? Babu.


Don haka ya kamata mutane su godewa Allah, wanda ya ƙaddara musu haihuwa bisa tafarkin da za su mori 'ya'yansu domin su amfani kansu da iyayensu da ma al'ummar da suke rayuwa a cikinta. Kuma ya zama wajibi ga iyaye su ɗauri aniyar kuɓutar da 'ya'yansu daga bala'o'i da masifu na wannan rayuwa.