1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Kasar Sin.

abba bashirAugust 8, 2005

Takaitaccen Tarihin Kasar Sin.

https://p.dw.com/p/BwXU
Chinas Currency.
Chinas Currency.Hoto: AP

Tarihin Kasar Sin.

Masu sauraron mu asalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawar farko a cikin shirin ta fito ne daga hanun Hussainin mai Lemu da kwakwa garin Kakumi na karamar hukumar Bakori ta jihar katsina a tarayar Nigeria.Mai sauararon namu cewa yayi yana so mu bashi tarihin kasar Sin.

Amsa: Kasahe da dama na yammacin turai sun mamaye kasar Sin tun daga shekarun 1644,kuma a wanan lokaci ne aka kafa dauloli a kasar.Bayan yakin duniya na biyu kasar Sin ta yi fama da yake yake na neman yanci daga turawan mulkin malakar kasahen yamma.Kasar Sin ta zamanto jamhuriyar mai cin gashin kanta a ranar daya ga watan Octoban 1949,kuma shugaba Mao shine daya daga cikin shugabanin na farko da suka yi fafutkar nemawa kasar yancin kanta.Kasar dai ta China mai hedkwata a Beijing a shekara ta 2002 an kiaysta cewa nada yawan alumma 1,284,303,705.kuma da za’a yi rabo na dai dai wadaida na irin arzikin da Allah ya horewa kasar kowane dan kasar zai sami dola $4,300.

A yankin arewa kasar ta Sin ta yi iyaka da kasahen Rasha da mangolia,a yankin kudu maso gabashi kasar Sin ta yi iyaka da kasahen Vietnam,Loas,Mynmar,Bhutan da Nepal.

Sai a kudanci inda kasar ta Sin ta yi iyaka da India,Pakistan,Afghanistan,da kuma Tjikistan.Kasar China nada fadin fadin kasa da yawansa ya kai fadin muraba’in kilomita 9,579,000.A wasu dokoki da aka kafa a shekara ta 1979,an haramtawa ma’uratan kasar ikon samun da fiye da daya saboda matsalar tattalin arziki,to sai dai kuma a 1988,an yiwa wanan tsarin doka sasauce,inda bayan shekaru hudu da samun ya mace aka amince a sake samun da namiji.A kasar dai ta Sin ana magana ne da harsuna da dama na kanan kabilu,to sai dai kuma harshen Wu shine harshen da aka fi amfani da shi a duka fadin kasar.

Kasar dai ta Sin an kasata izuwa laurduna 22,shugaban kasa Jiang Zemin shi ne shugaban kasa kuma shugaban rindinar sojin kasar.Kasar China Memba ce a kwamitin tsaron majalisar dikin duniya,da kuma bankin habaka tattalin arzikin kasahen Asia,APEC a takaici.

A shekara ta 1996 kasar Sin na dogara ne kachokan kann samun talafi daga kasahen ketare,inda a wanan shekara aka kiyasta cewa ta karbi taimako har na dola biliyan biyu da dubu dari shida daga kasahen duniya,fiye da kowace kasa ta duniya.Kasar China Allah ya albarkanci ta da ma’adania na karkashen kasa da suka hadar da Kwal,mai da kuma gas.Haka zalika China na daya daga cikin kasahen da suka dukufa wajen bunkasar aiyukan noma don ciyar da alumar kasa.Gwamnatin China ta amince da kafuwar addinia biyar da suka hadar da addinin musulunci,Budhisim,Protestanisima,Roman Catolisim,Toisim da dai sauran su.

Muna fata Hussaini mai Lemu da kwakwa na karamar hukumar Bakori a Nigeri ya gamsu da wanan amsa da muka bashi ta tarihin kasar Sin watau China.