1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

030511 Fatah Hamas

May 4, 2011

Shugabannin ɓangarorin Falasɗinu masu gaba da juna a yanzu sun ƙuduri kawo ƙarshen taƙaddama tsakaninsu don ciyar da yankinsu gaba

https://p.dw.com/p/118ls
Shugaba Mahmoud Abbas da jagoran Hamas Khaled Mashaal, a wata gawa da suka yiHoto: AP

San'ya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza da kuma Fatah wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mahmud Abbas wani ci gaba ne na samun masalaha tsakanin bangarorin biyu. Sanya hannu wanda jagoran Hamas Khalid Mashal da shugaban Falastinawa Mahmdu Abbas za su yi, za a yi shine a wani biki a birin Kairo. A Laraban da ta gabata ne dai a wani jawabin ba zata da shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya yi ya sanar da sulhu tsakaninsu.

A ƙarshen shekara ta 2006 mutumin da ya yi nasar a zaɓen majalisar dokokin Falasɗinu Isma'il Haniya, ya yi wata hira da gidan radiyon Isra'ila inda ya buƙaci ƙasashen Turai da Amirka da su amince da gwamnatinsa kada su biye wa farfagandar Isra'la, wanda ta yi watsi da nasar Hamas.

Verhandlungen zwischen Hamas und Fatah
Wakilin Hamas Musa Abu Marzuka da wakilin Fatah Azzam al-Ahmad waɗanda suka jagoranci samar da yarjejeniya a tsakaniHoto: picture alliance/dpa

"Ƙasashen da suka yi shekaru suna cewa basa mutunta ko wace gwamnati in ba ta demokraɗiyya ba. Yanzu muna buƙatarku ku amince da zaɓin al'ummar Falasɗinu, ta yadda nan gaba za su mutunta tsarin demokraɗiyya"

Cin zaɓen da Hamas ta yi a wacan lakacin dai ya zo da mamaki, inda Falasɗinawa suka nemi kawo ƙarshen jagorancin gwamnatin Fatah mai cike da cin hanci, da kuma gajiya da yadda take takarawa kan mamayar da Isra'ila ke yi musu. Daga nan sai shugaban Fatah Mahmud Abbas ya buƙaci jagoran Hamas ya kafa gwamnati, kana ya amince da Israi'a abinda zai kawo ƙarshen datsewar da Isra'ila ke yi wa yankin, da zimmar samun haɓakar tattalin arziki. Bayan zaman sasantawa da aka sha yi ba babu nasara, Abbas ya yi barazanar rusa majalisar dokoki da kiran wani sabon zaɓe.

"A cikin kundin tsarin mulki an bayyana cewa iko yana hannun al'umma. Don haka na ke roƙon ku mu koma fagen daga. Domin jama'a su yi zaɓi, domin jama'a sune alƙalai"

Nan take Mahmud Zahar mai ɗasawa da shugaban Hamas ya mai da martani.

"Ba za mu shiga zaɓen ba, ba za mu yarda da wannan canjin ba, idan Abbas ya gaji to ajiye mulkin, ya yi murabus"

Bayan waɗannan kalamai ba da jimawa ba aka fara fafatawa tsakanin Fatah da Hamas a zirin Gaza, inda mutane da yawa suka mutu kafin Hamas ta fatattaki dakarun Fatah daga Gaza.

Zwei Jahre Gazakrieg
Wata jatuma da yara ke kan buraguzan ginin da Isra'ala ta rusa harin da ta kai GazaHoto: DW

Abbas ya naɗa Salam Fayyad a matsayin sabon Farai minista, duk da cewa ya kyauta tsarin kungiyar Fatah, amma Fayyad bai cimma wani abun azo a gani ba a siyasance. A shekara ta 2008, Isra'ila ta kaddamar da yaki a Gaza inda ta hallaka mutane 1400. A wani abinda tace mai da martani ne ga hare-haren rokokin da Hamas ke cilla mata.

A ɗaya hannun kuwa an kasa ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa. Duk da cewa shugaban Amirka Obama ya sha alwashin kawon zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tun lokacin da aka zabe shi. Bayan shekaru biyu da rabuwa, yanzu a wannan karon ko za a samu nasarar cimma wani abun azo a gani, a dai dai lokacin da guguwar neman sauyi ke kaɗawa a ƙarshen Larabawa. Lokaci ne kawai zai nuna.

A ƙasa kuna iya sauraron sauti a rahoton da Usman Shehu Usman ya haɗa mana.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu