1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tallafawa Najeriya wajen shirya zaɓe na adalci

February 9, 2011

Yayin da ake ci-gaba da kamfen, an fara saka ayar tambaya game da sahihancin hukumar zaɓen Najeriya ta INEC bayan matakin da ta ɗauka na janye jerin sunayen 'yan takara.

https://p.dw.com/p/10El4
Hoto: Katrin Gänsler

A yayin da wata sa-in-sa ta kunno kai a ɓangaren shari'a na tarayyar Najeriya, inda alƙalin babbar kotun ɗaukaka ƙara ya kai ƙarar alƙalin-alƙalan ƙasar, dangane da batun ƙarin girman da aka yi masa, inda ya dangan ta hakan da siyasa da kuma cewa ba da kyakkyawar manufa aka yi masa ƙarin girman ba. Ita kuwa hukumar zaɓen Najeriya ta INEC ta yi amai ta lashe inda ta janye jerin sunayen 'yan takara, bayan da ta bayyana sunayen. Tuni dai wannan matakin da INEC ɗin ta ɗauka yake shan suka daga 'yan siyasa waɗanda suka ayar tambaya game da sahihancin hukumar.

A shirye-shiryen zaɓen ƙasar na watan Afrilu kuma, gwanmatin Jamus ta ce za ta tallafawa Najeriyar wajen cika burin da ta sanya a gaba na gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, abinda ta ce zai yi tasiri wajen wanzuwar zaman lafiya a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.

A ci-gaba da kamfen neman muƙamin shugaban Najeriya, shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo na ci-gaba da rangadin yankunan ƙasar.

Mun tanadar muku rahotanni game da waɗannan batutuwa. Na farko daga wakilanmu na Abuja, Ubale Musa da Uwais Abubakar Idris sai kuma Ado Abdullahi Hazzad daga Bauchi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal