1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar fraministan Italy

February 9, 2011

Ranar Laraba 9 ga watan Fabrairu ake sa ran miƙa buƙatar gurfanar da fraministan Italy, Silvio Berlusconi a gaban kotu bisa zargin yin lalata da wata matashiya

https://p.dw.com/p/10Dtu
'Yan zanga-zangar nuna adawa da take-taken BerlusconiHoto: Picture-Alliance/dpa

A ranar Laraba 9 ga watan Fabrairu ake sa ran cewa jami'an shigar da ƙara a ƙasar Italy za su buƙaci Framinista Silvio Berlusconi da ya fuskanci shari'a bisa zargin da ake masa na yin lalata da wata matashiya 'yar shekaru 17 da kuma taimaka mata ba akan ƙa'ida ba. Babban jami'in shigar da ƙara a Italy ya ce yana shirin neman gaggauta sauraron shari'ar da ake yi wa franinistan mai shekaru 74 da haifuwa akan zargin biyan kuɗi ga wata ma'aikaciyar gidan rawa domin ya yi lalata da ita. In har kuwa wannan mataki nasa ya samu ƙarbuwa za a buƙaci tsallaka matakin farko na shari'ar domin gaggauta yanke masa hukunci. Berlusconi dai ya musunta wannan zargi yana mai kiran hakan tamkar wani yunƙuri na tuɓuke shi daga kujerar shugabanci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu