1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saƙa tsakanin hukumar zaɓen Nijeriya da jam'iyyun siyasar ƙasar

February 8, 2011

Jam'iyyun siyasar Nijeriya sun ƙi amincewa da hukuncin hukumar zaɓe ta INEC a game da tsayar da canja 'yan takarar da suka gabatar mata da sunayensu a zaɓen watan afrilu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/10DZr
Rikici tsakanin INEC da jam'iyyun siyasar Nijeriya akan 'yan takaraHoto: DW/Katrin Gänsler

Jerin sunayen 'yan takarar zaɓen da hukumar zaɓe ta Nijeriya INEC a taƙaice ta fitar na ci gaba da haifar da cece-kuce da ma ta da jijiyar wuya tsakanin jam'iyyun siyasa da ma 'yan takarar, lamarin da ya sanya jam'iyyar adawa ta CPC ta mayar da martani tare da nuna cewar ba zata saɓu ba a ce wai hukumar zaɓen ce zata zaɓa mata waɗanda zasu yi mata takara. To sai dai kuma a inda take ƙasa tana dabo shi ne yadda jam'iyyun siyasar suka canza sunayen 'yan takararsu da suka cimma nasarar zaɓen fid da gwani suka maye gurbinsu da wasu 'yan takarar daban da suka miƙa sunayensu ga hukumar zaɓen ta ƙasa, wadda a nata ɓangaren ta ce faufau ba zata lamunta da hakan ba. Domin jin ƙarin bayani sai a saurari rahotannin wakilanmu a can ƙasa, haɗe da hira da Dr. Mohammed Zayyanu Umar masanin siyasa a jami'ar Usmanu Ɗan Fodio dake Sakkwato.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal