1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080211 Weltsozialforum Afrikatag

February 8, 2011

Duk da matsaloli na shirye-shirye da aka fuskanta wajen gudanar da ranar ta Afirka, ɗaruruwan mutane sun hallara a jami'ar Sheikh Anta Diop dake birnin Dakar.

https://p.dw.com/p/10Cpw
An cashe a taron na ranar AfirkaHoto: DW/Renate Krieger

An gudanar da ranar Afirka a gun taron ƙasashen duniya kan kyautata zamantakewar al'uma da a babban birnin ƙasar Senegal wato Dakar. Duk da matsalolin shirye-shirye da aka fuskanta wajen gudanar da ranar ta Afirka, duk da haka dai ɗaruruwan mutane ne suka hallara a jami'ar Sheikh Anta Diop dake a yammacin babban birnin na Senegal, inda fitattun 'yan siyasa suka gabatar da jawabai game da nahiyar ta Afirka.

An gudanar da ranar ta Afirka ne kuwa da nufin yin ƙarin bayani tare da muhauwarori akan batutuwan da suka shafi nahiyar misali kan wani babban taro game da bukukuwan cikar shekaru 50 da samun 'yancin kan ɗaukacin ƙasashen Afirka ko alaƙa tsakanin waɗanda suka yi ƙaura da ci-gaban ƙasa.

Mamadou Kann ɗan ƙasar Mauritaniya ne dake kula da dangantakar ƙetare na wata ƙungiyar yaƙi da cin zali. Wannan dai shi ne karon farko da ya halarci taron masu adawa da manufofin haɗakar duniya, ya nuna rashin gamsuwarsa.

Weltsozialforum WSF World Social Forum 2011
Manoma kamar Armando daga Gini-Bisau na daga cikin mahalarta taronHoto: DW/Renate Krieger

"Mun ga wasu abubuwa na ɓacin rai a ranakun farko. Babu isasshiyar sadarwa da za ta sauƙaƙa wa mahalarta taron yin rajista. A dole ƙungiyoyin waɗanda aka ci zarafinsu kamar na mu, da za su shiga taruka na musamman, sun biya kuɗin halartar taron. Ta haka ba za a iya sauraronmu musamman a tsakanin ƙungiyoyin da ke a nan."

An sha fuskantar matsalolin gudanarwa

Hatta su kansu waɗanda suka ƙirƙiro wannan taron sun amsa cewa taron na su kan fuskanci matsaloli na shirye-shirye, kamar yadda ya faru a lokacin ranar ta Afirka, inda wani gungun mutane kai tsaye suka ce sun kafa wata ƙungiyar duba muradun Afirka. Allioune Tine shi ne shugaban ƙungiyar RADDHO ta kare haƙin ɗan Adam a Senegal, ya ce an kafa sabuwar ƙungiyar bisa ci gaban Afirka.

"Wannan nahiya ba matalauciya ba ce. Tana da ɗinbim ma'adanan ƙarƙashin ƙasa da ƙasa mai faɗin gaske. Saboda haka ya kamata a sake tunani. Mun ga yadda ƙasashe 'yan jari hujja suka kai iyakarsu sakamakon rikicin kuɗi na shekarar 2008. A lokaci ɗaya wasu ƙasashen sun farfaɗo ta hanyar amfani da ƙarfinsu da kuma basirarsu."

Manufar sakarwa kasuwanni mara ita ce mafita

Abdoulaye Wade Präsident vom Senegal Dakar
Mai masaukin baƙi Abdoulaye Wade mai goyon bayan tsarin jari hujja neHoto: picture-alliance/dpa

Shugabannin siyasa ma sun kasance a taron na ranar Afirka. Baya ga masu adawa da shirin Globalisation, shi ma shugaban Senegal Abdoulaye Wade ya yi magana game da gano hanyar warware matsalolin duniya. Mai masaukin baƙin wanda ɗan goyon bayan manufar jari hujja ne cewa yayi.

"Ni mai sassaucin ra'ayi ne. Saboda haka nake goyon bayan tsarin tattalin arziki dake tafiya daidai da halin da ake ciki a kasuwanni, amma ba wanda hukuma ke tsarawa, wanda kusan duk sun rushe saboda an ɗora su akan wani gurgun ginshiƙi."

Shi ma tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya halarci taron na ranar Afirka, inda a jawabinsa ya yi kira ga ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe masu tasowa. Ya ce ya kamata Brazil ta kasance ƙawar Afirka amma ba wata daula da za ta yi wa nahiyar babakere ba.

"Afirka za ta iya samun ci-gaban tattalin arziki da kyautata jin daɗin al'umarta haɗe da girke demokuraɗiyya da samun faɗa a ji a duniya, ba tare da sauran ƙasashen duniya sun yi mata katsalanda ba. Afirka mai yawan al'uma miliyan 800 da ɗinbim arzikin ƙarƙashin ƙasa, tana da kyakkyawar makoma."

To sai dai wasu daga cikin mahalarta taron na saka ayar tambaya game dangantaka tsakanin ƙasashe masu tasowa, domin China da Brazil na ƙoƙarin ci da gumin nahiyar ta Afirka domin cimma muradun kansu.

Mawallafa: Renate Krieger/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu