Harin Filin Jirgin Saman Mosko
February 8, 2011Shugaban wata ƙungiyar tawaye a checheniya ya fito ya ɗauki alhakin dasa bama-baman da suka yi sanadiyar hallakar wasu mutane 36 a filin jirgin saman Mosko a watan Janairun da ya gabata.
Doku Umarov, wanda ke ɗaya daga cikin waɗanda ke ta gwagwarmaya tun daga farkon yaƙin Checheniya a 1994, ya ce shi ya bada umurnin gudanar da ƙunar baƙin waken da ya afku a filin jirgin.
A jawabin da ya yi ta vidiyo, a wani shafi na yanar gizo, Umarov ya yi barazanar kai sabbin hare-hare kuma, domin cimma burin sa na neman damar mayar da yankin Caucasus da ke Rasha, 'yancintacciyar ƙasa mai amfani da tsarin mulkin musulunci. kawo yanzu dai masu gudanar da binciken a Rasha sun ce wani mai shekaru 20 da haihuwa daga yankin na Caucasus ne ake zargi da ƙunar baƙin waken.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu