1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

070211 Auftakt Weltsozialforum 2011

February 7, 2011

A ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu ƙungiyoyoni masu ra'ayin gurguzu suka fara taronsu a birnin Dakar na ƙasar Senegal.

https://p.dw.com/p/10CNW
Mahalarta taron ƙungiyoyin 'yan gurguzuHoto: AP

Dubun dubatan jama'a ne suka hallara a birnin Dakar na ƙasar Senegal a ranar Lahadi yayin bukin buɗe taron ƙungiyoyin masu ra'ayin gurguzu a duniya, wanda ake sa ran zai mai da hankali akan tsarin zamewar duniya tamkar gari guda da kuma halin da ke wakana a ƙasashen arewacin Afirka cikinsu har da Masar da Tunisiya.

Kimanin mutane dubu 30 ne suka hallara a gaban babban masallacin birnin Dakar na ƙasar Senegal yayin buƙin buɗe taron ƙungiyoyin masu ra'ayin gurguzu a duniya.Taron na kwanaki shida da ake gudanarwa domin nuna adawa da tsarin zamewar duniya tamkar gari guda wato "globalisation" shi ne irinsa na biyu da ke gudana a nahiyar Afirka.

Babbar ɗawainiya ga Afirka

Taron wannan shekara da zai gudana har ya zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu zai mai da hankali ne akan matsalar da ke tattare da tsarin jari-hujja. Waɗanda suka shirya taron na sa ran samun halartan mutane dubu 50. Mafi yawan masu nuna adawa da tsarin zamewar duniya tamkar gari guda da za su je birnin na Dakar na ɗaukar taron da muhimmacin gaske kasancewar Afirka ce ta karɓi baƙoncinsa.

Babouna D'Akite daga ƙasar Mauritayniya wanda ya shafe shekaru yana zaune a birnin Dakar inda yake aiki domin taimaka ma waɗanda suka yi gudun hijira daga ƙasarsa ta asali na daga cikin mahalartan wannan taro. Abin da ke da muhimmcani a gare shi shi ne tattauna batun 'yan gudun hijira.

Ya ce: "Afirka za ta ɗauki babbar ɗawainiya yayin wannan taro. Abin da ke da muhimmaci gun wannan taro shi ne ƙirƙirar da duniya mafi inganci da kuma bayyanar da matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka."

Joao Sanha wanda manomi ne daga ƙasar Guinea-Bissau shi kuma ya je birnin na Dakar ne domin ba da labarin yadda aikin noma yake a ƙasarsa.

Weltsozialforum WSF World Social Forum 2011
Joao Sanhá manomi daga Guinea-BissauHoto: DW/Renate Krieger

Yace "Muna rashin isassun kayan aikin noma a Guinea-Bissau kuma ba mu samun ci gaban tattalin arziƙi. Muna rayuwa ne hannu baka hannu ƙwarya. Muna buƙatar kwararru a ƙasarmu. Akwai injiniyoyi da dama da ke aiki a ƙasashen ƙetare . A saboda haka gwamnati na buƙatar mai da hankali wajen tabbatar da cewa waɗannan ƙwararru sun dawo gida."

Goyon bayan juyin-juya-hali a Tunisiya da Masar

Weltsozialforum WSF World Social Forum 2011
Evo Morales na Boliviya yayin jawabinsaHoto: DW/Renate Krieger

A dai wannan karon za a tafka muhawara ne akan juyin-juya-halin da ke wakana a ƙasashen Masar da Tunisiya. Akan wani dandamali da ya tsaya tare da shugabannin taron, a gaban jami'ar Cheikh Anta Diop Shugaban Boliviya, Evo Morales ya yi jawabi inda yake cewa:

"Ya ku 'yan'uwana maza da mata a sannu a hankali za mu kawar da tsarin jari-hujja in har muka tinkare shi. Muna sheda abin da ke aukuwa a Masar. Na kuma yi imanin cewa za a tayar da irin wannan bore a sauran ƙasashen Larabawa domin nuna adawa da tsarin jari- hujja na ƙasar Amirka. Ba za a iya dakatar da wannan juyin-juya- halin ba duk da kuwa makuɗan kuɗaɗen da Amirka ke turawa domin murƙushe shi. Na yi imanin cewa tsarin gurguzu shi ne kawai maganin wannan matsala amma ba danniya ba."

Shi kuma Alexis Passadakis jami'in ƙungiyar ATTAC da ke Jamus ya bayyana juyin-juya-halin da ke wakana a arewacin Afirka tamkar abin da ya dace.

Ya ce: "Abin da ke faruwa a halin yanzu a ƙasashen Tunisiya da Masar alama ce da ke nuni da cewa akwai yiwuwar ɗaukar mataki na daban da ya haɗa da kare tsarin gurguzu da dimukuraɗiya. Abin takaici shi ne yadda har yanzu waɗanda su ne ummul haba'isin wannan matsala ke ci da jan ragamar mulki."

Mawallafiya: Renate Krieger/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal