1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen raba gardama a kudancin Sudan

February 7, 2011

Alummar Kudancin Sudan sun fara jin ƙanshin sakamakon zaɓen da suka kaɗa na raba gardama wanda ake sa ran zai goyi bayan ɓallewar yankin kudanci daga Arewacin kasar domin kafa ta su 'yantacciyar ƙasar.

https://p.dw.com/p/10Brn
Magoya bayan ɓallewar Kudancin SudanHoto: DW/Schlindwein

Hukumar kula da zaɓen kudancin Sudan, ta ce za ta sanar da sakamakon zaɓen raba gardamar a yau litini da misalin ƙarfe 11 agogon Sudan wato ƙarfe takwas ke nan agogon GMT a babban birnin Khartoum.

Hukumar za ta gabatar da sakamakon ne a hukumance bayan da sakamakon wucin gadin da aka fitar ranar 30 ga watan Janairu ya nuna cewa kusan kashi 99 cikin 100 sun goyi bayan ɓallewar ƙasar.

A lokacin sanar da sakamakon dai, Shugaban hukumar zaɓen, Mohammed Khalil Ibrahim zai gabatar da sakamakon kana ya miƙa shi zuwa shugaba Omar Al Bashir da shugaban yankin Kudanci, Salva Kiir a fadar shugaban ƙasar.

A yanzu haka dai Khartoum da Juba suna da ƙasa da watanni shidda domin su sassanta batutuwan da suka rage tsaƙanin su, waɗanda suka haɗa da shata iyakokinsu da makomar yankin Abiye mai arziƙin man fetur, da raba kuɗaɗen shiga na mai, sai kuma takardun kudi da bashin da ƙasar ta ciwo, waɗanda kuma a ke fatan kammalawa kafin tara ga watan Yuli, ranar da kudancin zai gudanar da bukin samun 'yancin kai.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Abdullahi Tanko Bala