1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cijewar tattaunawar rikicin Darfur na Sudan

December 31, 2010

Gwamantin Sudan ta ce ba za ta ci gaba da tattaunawa da 'yan tawayen Darfur ba matiƙar ba a ɗora daftarin yarjejeniya a kan teburi ba.

https://p.dw.com/p/zrpY
'yan tawayen JEM na Darfur a zauren tattaunawa na DohaHoto: AP

Gwamnatin Sudan ta janye wakilinta a taron sasanta rikicin yankin Darfur da ke gudana a birnin Doha tsakaninta da 'yan tawayen wannan yanki. Mai magana da yawun fadar mulki Khartum wato Ghazi Salaheddine ya ce rashin samun ci gaba mai ma'ana tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan zama kan teburin tattaunawa ne ya sa su ɗaukan wannan mataki. Kwanaki 12 jami'an gwamantin Sudan da kuma 'yan tawayen JEM suka shafe suna tattaunawa a babban birnin Qatar ba tare da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu ba.

Ita dai gwamanti ta yi alƙawarin ci gaba da bayar da haɗin kan da ake bukata- domin sansanta rikicin yankin Darfur da ya jefa yankin na yammacin Sudan cikin yaƙin basasa. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa aƙalla mutane 300.000 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu ƙarin mutane miliyon uku suka yi gudun hijira a matsin shekaru bakwai da aka shafe ana gwabza faɗa tsakanin ƙungiyoyin 'yan tawaye daban daban da kuma dakarun gwamanti.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala