1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amincewar Burazil da 'yancin ƙasar Falasɗinu

December 30, 2010

Shugaban Falasɗinawa zai ziyarci Burazil, don nuna murnar sa kan amincewa da yancin su, wanda Burazil ɗin ta yi.

https://p.dw.com/p/zrNG
Shugaban Falasɗinawa, Mahmoud AbbasHoto: AP

Ana saran shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas zai kasance ɗaya daga shugabannin da ke hallartar rantsar da shugabar ƙasar Brazil Dilma Russeff. Abbas a ziyarar ta sa zai kafa tubalin ofishin jakadancin Falasɗinawa a ƙasar. A farkon wannan shekaran ne ƙasar Brazil, tace ta amince da yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, a dai-dia iyakar ta da aka amince a shekara ta 1967. Ƙasar ta Burazil tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka amince da 'yancin ƙasar Falasɗinu a watannin nan. Shirin Amirka na sasanta Yahudawa da Falasɗina ya gamu da cikas, bayan da gwamnatin Yahudawa suka ƙi su katse gina matsugunansu a yankunan Falasɗinawa da suka ƙwace da ƙarfin bindiga.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Alyiu