1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Adawa A Bailorushiya

Tijani LawalDecember 29, 2010

Har dai ya zuwa halin da muke ciki yanzu ana ci gaba da tsare ɗaruruwqan 'yan adawa da gwamnati a Bailorushiya.

https://p.dw.com/p/zr7r

An tsare 'yan adawar ne sakamakon adawar da suka nunar akan maguɗin zaɓen da gwamnatin shugaba Lukashenko ta caɓa a tsakiyar wannan wata. Tuni dai magoya bayan 'yan adawar suka yi kiran ɗaukar matakai na nuna zumunci ga fursunonin dake tsare.

A lokacin da suke jerin gwano 'yan zanga-zangar sun yi kira tare da ihun cewar Allah Ya ja ran ƙasar Bailorushiya kuma Yayi awon gaba da Lukashenko. Hakan dai ya faru ne kai tsaye bayan zaɓen, inda dubban masu zanga-zanga suka runtuma kan titunan Minsk fadar mulkin ƙasar. Rundunar sa kai sun yi amfani da kulake don yi wa masu zanga-zangar ɗan karen duka. Wani da ake kira Siarzhuk Semianiuk ya shirya shiga a dama da shi a zanga-zangar, amma bai samu kafar yin haka ba sakamakon matsayinsa na mai sa ido akan zaɓen a birnin Minsk.

"Mun kammala ayyukanmu a makare a wajejen ƙarfe ɗaya na dare. Kuma a wannan lokaci tuni aka fatattaki mutane. Da farko mun shiga ruɗu da rashin sanin tabbas. An yi wa mutane duka mu kuma ba ma nan."

Sama da 'yan zanga-zanga 600 aka tsare a ranar 19 ga wata, kuma suka wayi gari a gidajen kurkukun Minski dake da raɗaɗin sanyi. A tashar telebijin ta gwamnati an gabatar da masu zanga-zangar tamkar mashaya dake samun goyan baya daga ƙasashen yammaci. Kuma ko da yake wasu daga cikin al'umar ƙasar sun yi Allah Waddai da zanga-zangar, amma kuma akwai mutane irinsu Semianiuk dake bayyana ra'ayinsu kamar haka:

"Kashe gari muka samu labarin cewar an tsare ɗaruruwan mutane a gidajen kurkuku ko kuma an gabatar da wasu daga cikinsu gaban kuliya. Suna buƙatar taimako, amma ba mu da wani zaɓi. Mu da ba a tsare mu ba wajibi ne mu yi bakin ƙoƙarinmu wajen taimaka musu."

A dai halin da ake ciki yanzun, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bikin jajibirin sabuwar shekara Semianiuk da sauran masu kai gudummawa sun lashi takobin jan daga gaban gidan kurkukun da fursinonin ke tsare har sai sun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. A ɗaya ɓangaren kuma ana daɗa samun cikakkun bayanan dake nuna hanyoyin da gwamnatin Lukashenko ta bi don aikata maguɗi a zaɓen. Natalia Vasilevitch jami'ar sa ido ce a wata rumfar zaɓe dake birnin Minsk ta kuma yi bayani tana mai cewar:

"Akwai saɓani dangane da yawan masu zaɓe da adadin ƙuri'un da aka kaɗa. Misali dai kimanin mutane 1300 ƙuri'un zaɓen suka shiga hannunsu, amma a bayanan da aka rubuta sai aka ce wai adadin ya kai 1952. Kamar dai yadda labari ya zo mana daga baya, wai dukkan waɗannan ƙuri'un na ba da goyan baya ne ga Lukashenko."

Bayan sake ƙididdigar ƙuri'un a wannan rumfar zaɓen sai aka ba wa Lukashenko kashi 80 cikin ɗari a hukumance. Amma fa ainihin goyan-bayan da shugaban ya samu a birnin Minsk gaba ɗaya bai wuce kashi 40% ba. Lamarin da ba a bayyanar a tashar telebijin ta ƙasa ba, sai dai daga baya ya riƙa bayyana ta yanar gizo.

Mawallafi:Olga Kohl/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu