1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan tsaro a filin saukar jiragen sama na Dusseldorf

Sadissou YahouzaDecember 29, 2010

Gwamnatin Jamus ta yi watsi da sabbin makakan tsaro a filin saukar jiragen samar Dusseldorf

https://p.dw.com/p/zqyX
Daraktan filin saukar jiragen sama na DusseldorfHoto: picture-alliance/ dpa

Babban daraktan filin saukar jiragen sama na Dusseldorf da ke nan Jamus ya gabatar da wasu shawarwari da zumar ƙarfafa matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama na Jamus.

Christoph Blume ya ce ta la´akari da yadda a ka kasa shawo kan matsalar tsaro , nan gaba kamata ta yi, a dinga ware fassenjoji rukuni -rukuni.

To saidai wannan shawara ta ci karo da mummunar adawa daga gwamnatin Jamus.

A yayin da ta ke hurucu akai, ministar suhurin kasar Jamus, Sabine Leutheusser-Schnarrenberger, ta ce wannan mataki ba zai aikatu ba, domin zai cusa wariya tsakanin fasenjoji, kuma ya sabawa ƙa´idodin Ƙungiyar Tarayya Turai da na Jamus game da batun nuna adalci tsakanin ko wane jinsi na bani adama, ba tare da la´akari da addininsa, ƙabilarsa ko kuma launin fatarsa ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu